Boko Haram Sun Yi Ikirarin Kafa Daula A Geidam Ta Jihar Yobe

0
220

Boko Haram Sun Yi Ikirarin Kafa Daula A Geidam Ta Jihar Yobe

Rahotanni daga garin Geidam dake jihar Yobe na tabbatar da har zuwa tsakiyar ranar yau Asabar mayakan Boko Haram na cikin garin bayan harin da suka kai a yammacin jiya juma’a da misalin karfe 5:30.

Wani mazaunin garin kuma shaidar gani da ido yace har ya zuwa yau da rana mayakan na cikin garin dauke da makamai da kuma sabbin motocin yaki da suka yi amfani da su wajen kai farmaki garin.

Mutumin ya kara da cewa mayakan solar kai hari yau da protected tare da cinna wuta a wasu gine gine da kuma fasa shaguna suna kwashe abinci, yayin da akasarin mutanen garin suka nemi mafaka a cikin gidajen su, wasu kuma suka fara sulalewa ta hanyar daji suna barin garin.

Shaidun solar tabbatar da samun wata takarda da ‘yan ta’addan suke ikirarin kwace iko da garin, inda suka yi ikirarin maida garin cikin garuruwan da ke karkashin daularsu.

What's On Your Mind?