Boko Haram Sun Sake Kai Farmaki Maiduguri

- Advertisement -

Boko Haram Sun Sake Kai Farmaki Maiduguri

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Wasu maharan da ake kyautata zaton Boko Haram solar cinna wa wasu gidajen jama’a wuta, a farmakin da suka kai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da yammacin ranar Talata.

Bugu da kari, ana jin karar harbe-harben manyan bindigogi masu sarrafa kansu tare da karar ababe masu fashewa a kowane bangaren birnin, musamman yankin unguwar Jiddari Polo.

Har wala yau, wakilinmu ya labarta mana cewa akwai gumurzu mai zafi da ya kaure tsakanin sojojin Nijeriya da maharan da ake sa ran yan kungiyar Boko Haram ne a yankunan Molai da Jiddari duk a cikin birnin Maiduguri.

Yanayin ya jawo jama’a a wadannan unguwannin sai cin karo suke da juna a lokacin da suke gudun ceton rai a birnin a cikin yanayi mai cike da demuwa.

“Akalla wasu abubuwa masu karar gaske ne suka tarwatse Maiduguri, tare da karar harbe-harben manyan bindigogi ke tashi yanzu haka, a lokacin da jama’a ke guduwa suna barin gidajen su a Damboa da Outdated GRA.” Ta bakin majiyar tsaro.

Wani magidanci wanda ya zanta da wakilinmu ta hanyar wayar tafi-da-gidanka, ya bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali sakamakon wannan harin.

“A halin da ake ciki yanzu ina cikin hadari. Saboda yanzu haka ba zan iya zuwa gida ba. Kana jin karar harbe-harben bindigogi yana tashi kusa da inda nake.” In ji shi.

- Advertisement -