Boko Haram sun kashe ‘yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno

0
51

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun afka Chabal da wasu anguwanni dake karkashin karamar hukumar Magumeri a ranar Lahadi da rana sannan sun kashe wasu ‘yan sanda guda biyu kafin su yi garkuwa da wasu biyu.

Kamar yadda wasu suka sanar da Vanguard, ‘yan ta’addan sun kwace wasu motocin sintiri guda biyu sannan suka banka wa daya wuta a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri titi mai tsawon 35km arewa da babban birnin jihar.

Al’amarin ya faru ne bayan sababbin hafsoshin sojin Najeriya da sun kai ziyara Maiduguri, inda suka kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara da Shehun Borno, Abubakar Garbai Elkanemi don neman hadin kansu wurin kawo karshen rikici a jihar.

Sai ga ‘yan ta’adda sun kai farmaki jihar a yau Lahadi.

Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno

(*2*)

A wani labari na daban, wasu matasa sun kai wa kwamishinan ayyukan jihar Ondo, Saka Ogunleye, farmaki yayin da rikicin cikin jam’iyyar APC yake kara ruruwa a tsakanin ‘yan jam’iyyar.

Ana zargin karamin ministan Niger Delta, Chief Tayo Alasoadura da tura matasan don su kai wa kwamishinan farmaki.

Dama rikici ya balle tsakanin kwamishinan da karamin ministan, wanda ake zargin haka ne makasudin da ya sanya ministan sanya matasan kai wa kwamishinan farmaki a garin Iju ana tsaka da taron rijista da tabbatar da ‘yan jam’iyyar APC.

What's On Your Mind?