Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Gaidam A Yobe – Danmajalisar Yankin

0
144

Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Gaidam A Yobe – Danmajalisar Yankin

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

dan majalisa mai wakiltar Geidam, Yunusari da Bursari a zauren majalisar wakilai ta kasa, Hon. Lawan Shettima, ya bayyana cewa babu gaskiya a kan cewa an kori Boko Haram daga garin Geidam, bilhasali ma su ne ke iko da garin.

Bayanan da ke fitowa daga garin Gaidam a jihar Yobe solar bayyana cewa mayakan Boko Haram suna ci gaba da mamaye garin bayan harin da suka kai, wanda ya kai ga kafa tutarsu a wasu sassan garin.

Mayakan kungiyar solar rusa na’urorin sadarwa, al’amarin da ya tilasta jama’a kauracewa garin.

Geidam shi ne mahaifar mukaddashin Safeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba.

Mazauna garin solar shaida wa wakilinmu cewa har a lokacin hada wannan rahoton, ‘yan ta’addan suna cikin garin tare da kafa tutocin su a wasu unguwani a garin da bi gida-gida suna yi wa mutanen gari wa’azin yarda da akidarsu.

Sabanin sanarwar da Daraktan yada labarai na rundunar sojojin Nijeriya- Mohammed Yerima ya fitar, wanda ya ce solar fatattaki Boko Haram daga Gaidam, yayin da Hon. Lawan Shettima ya ce, “A hukumance nake bayar da tabbacin cewa wadannan ‘yan ta’addan solar mamaye Geidam. A faifan bidiyo da hotuna za ka rinka ganin yadda suke yawo layi-layi tare da kona duk abinda suka ci karo dashi.”

Hon. Shettima ya ce, “Al’ummar mazabata suna karkashin mamayar Boko Haram sama da awanni 24 ba tare da wani dauki ba, ballantana wani ingantaccen kalubale ba.”

Gwamna Mai Mala Buni ya bukaci a samar da daukin soji na musamman wajen bayar da cikakken tsaro a Geidam da sauran garuruwan da ke kan iyaka da jihar Borno.

Gwamna Buni ya sanar da hakan a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun Kakakinsa, Mamman Mohammed, tare da jajanta wa al’ummar Gaidam wadanda ibtila’in ya rutsa dasu.

What's On Your Mind?