Boko Haram, Jagororin Garkuwa Da Mutane A Nijeriya

0
122

Boko Haram, Jagororin Garkuwa Da Mutane A Nijeriya

Nijeriya ba ta taba shaida mummunar yanayi na garkuwa da mutane a arewacin Kasar ba, sai bayan bayyanar asharariyar kungiyar Boko Haram, wadda a kullum ke fakewa bayan koyarwar addinin Musulunci. Wanda hakan, ya jaza yi wa addinin mummunan kallo a cikin gida da waje.

Kamar yadda aka ambata a baya cewa, sai cikin Shekarar 2009 ne aka fara yin kwalli da ta’adar garkuwa da mutane a arewacin Nijeriya, lokacin da almajiran Muhammad Yusuf (Allah Ya kara nauyin kasa) suka fara farmakar hukuma da sauran jama’ar gari, da sunan jihadin musulunci, duk da cewa shi addinin, ya yi gabas ne, su kuma solar runtuma zuwa yamma a sukwane.

Garkuwa Da Daliban Chibok, 2014

Ba ya ga garkuwa da mutane da “yan Kungiyar ta Haramun (Boko Haram) su ka fara cikin Shekarar 2009, sai ya zamana cewa, ba a taba yin wani garkuwa da mutane a wannan Kasa ta Nijeriya gabanin Shekarar 2014, irin wanda a ka yi a garin Chibok, wanda ya ja-hankalin kafofin yada labarai na cikin gida da na waje tamkarsa ba.

A cikin Shekarar ta 2014, daskararriyar Kungiyar ta Boko Haram, ta sami nasarar kutsawa ne har cikin makarantar Sakandiren “yan mata ta Chibok, tare da taso keyar dalibai mata kimanin dari biyu da saba’in da shida (276) da sunan solar yi garkuwa ne da su.

Bayan sato wadancan yara ne, sai Kungiyar ta BH ta nemi da a ba ta kudin fansa. Bugu da kari ma, solar nemi gwamnati da ta sako musu irin mutanensu da ake tsare da su a gidajen gyaran hali (kurkuku).

Daga Haduran Boko Haram Bayan Garkuwa Da Mutane

Babu shakka akwai banbanci a tsakanin irin garkuwa da mutanen da Barayin Daji ke yi, da irin na “yan Kungiyar ta Boko Haram. Su “yan ta’addar daji, solar fi karkata ne, na a ba su kudi. Sukan ma nemi a sako musu mutanensu, ko yunkurin yin lalata da irin wadanda su ka sato, Boko Haram fa?.

Daga sharrin masu garkuwa da mutane bangaren Boko Haram shi ne, da farko dai, duk wani abu da sauran Kungiyoyin satar mutane da sunan garkuwa da su ke yi, ita ma kungiyar Boko Haram na yi. Dadin dadawa, cikin irin mutanen da “yan Boko Haram din su ka sato, su na koya musu yin kunar-bakin-wake ne ta karfi. Su na ma koya musu sarrafa bindugu da kai hare-haren ta’addanci ga al’umar Kasa.

Daga ma fi illar ta’adar Boko Haram bayan sato mutane musamman mata shi ne, tilasa musu aurensu. Uwa uba, tilasa su shiga cikin addinin musulunci ta karfi da yaji. Ina ne aka ce a yi haka cikin koyarwar musulunci?. Sau da yawa a yau, musulmi ne ke zuwa da wasu irin miyagun manufofin da wadanda ba musulmi ba ke tuhumarsu da ayyukan ta’addancin da a zahirance ta’addancin ne!. Duk da cewa akasarin al’umar musulmi, suma ba su aminta da irin wadannan ayyuka na ta’addancin ba.

Daliban Chibok : Amina Ali Nkeki

Amina Ali Nkeki, na daga cikin daliban Chibok 276 da aka yi awon-gaba da su daga waccan makarantar sakandiren ta Chibok a Shekarar 2014. Ko da yake, “yan mata 57 solar sami subutowa daga hannun masu garkuwar, bayan wasu “yan Watanni da sace su. Kimanin 219 na adadin daliban, solar cigaba ne da zama a hannun “yan kungiyar ta Boko Haram har na tsawon wasu Shekaru.

Kungiyar hadin-gwiwa ta “yan sintiri ne su ka sami nasarar gano Amina Ali, da ita da jaririn da ke hannunta da bai wuce Watanni hudu (four) ba a Duniya, sai kuma wani mutum kato dan Boko Haram, da ake kira da M. Hayatu, wai a matsayin mijinta! Shin, akwai wata makarkashiya da za a yi wa musulunci sama da irin wannan iskancin?.

Garkuwa Da Daliban Dapchi, 2018

Shekaru hudu (four) da garkuwa da daliban Chibok, sai kuma al’umar Nijeriya su ka sake wayargari da cewa an sake yin wata garkuwar ma da wasu dalibai mata. Sakandiren Chibok, na cikin jihar Borno ne, ita kuma ta Dapchi, na a cikin jihar Yobe ne. Sai ya zamana ranar 19 ga Watan Fabarairun Shekarar 2018 (February 19, 2018) ne misalin karfe biyar da rabi na yamma (5:30pm), masu garkuwa da matan, su ka kutsa-kai har cikin makarantar, su ka kwaso dalibai mata har guda dari da goma (110), masu Shekarun haihuwa tsakanin 11 zuwa 19.

Babu shakka, akwai wasu tambayoyi da ya dace a ce hukumar Soji ta Kasa ta amsa su, karkashin waki’ar sace “yan Matan na Dapchi. Rashin titse manyan jami’an tsaro na su amsa irin wadancan tambayoyi, na daga dalilan da za a iya cewa, shawo kan irin wadannan miyagun ta’adodi na da matukar wuya.

Bayan sace daliban na Dapchi, gwamnatin tarayya ta jibge nau’i iri daban-daban na jami’an tsaro, don a samu a kubuto da su daga hannun “yan ta-da kayar-bayan. Labari ya zo cewa, ranar da aka yi wannan garkuwa, dalibai 5 cikin wadanda a ka sacen, solar mutu. Kwatankwacin na Chibok, suma 6 daga cikinsu solar rasu, kamar yadda Amina Ali ta labarta.

Bayan Wata guda (daga Fabarairu zuwa Mac, 2018) da sace wadannan dalibai na Dapchi, an sami nasarar dawowa da su, ban da yarinya guda da ake kira da Leah Sharibu, wadda “yan ta’addar su ka ki sako ta, saboda ta ki yarda ta ajiye addininta, ta rungumi musulunci! Da alama dai wadannan “yan Kungiyar ta Boko Haram, suna so ne su kyalayar da duk wata kima da Addinin Musulunci ke da, a idon Duniya.

 

What's On Your Mind?