Boko Haram: Gwamna Buni Ya Sake Garzayawa Shalkwatar Sojojin Nijeriya 

- Advertisement -

Boko Haram: Gwamna Buni Ya Sake Garzayawa Shalkwatar Sojojin Nijeriya 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya a jam’iyyar APC na kasa, Hon. Mai Mala Buni, ya gana da Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Ibrahim Attahiru domin tattauna batun tsaron da ya addabi jihar, ranar Laraba.

Gwamna Mai Buni ya bayyana cewa ganawa da shugaban rundunar sojojin ya zama dole wanda hakan zai bayar da damar lalabo ingantattun matakan bin wajen samun nasarar shawo kan kalubalen tsaron da ya addabi jihar.

Gwamna Buni ya bayyana hakan a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai a ofishin sa, Mamman Mohammed, wanda aka raba wa manema labarai ciki har da Management A Yau a Damaturu, yayin da ya fara da bayyana cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen ganin ta bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya da hadin gwiwa a yaki da matsalar tsaron.

Bugu da kari, ya ce hakan ya zo biyo bayan sabbin hare-haren da kungiyar ke ci gaba da kai wa a garuruwan da ke kan iyakar jihar, ya kara da cewa, ya ziyarci shugaban rundunar sojojin Nijeriya ne domin neman dauki tare da daukar dukan matakan da suka dace wajen kare jihar daga barazanar yan ta’addan.

Buni ya ce, “Sannan ta bangarenmu, gwamnatin jihar za ta bayar da dukan goyon baya da hadin gwiwar da ya dace ga jami’an tsaro a kokarin inganta sha’anin tsaro a jihar.” In ji Gwamna Buni.

Har wala yau kuma, Gwamna Mai Mala Buni ya yi kira ga al’ummar jihar su bai wa jami’an tsaro goyon bayan da ya dace tare da kada baki ya ce, “wannan nauyi ne da ya hau kan kowa a halin da ake ciki na yaki da matsalar tsaro.”

Haka zalika kuma ya yi kira na bai daya ga jama’ar jihar su ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro ga aikin samar da tsaro a kan iyakokin jihar don kakkabe gyauron Boko

- Advertisement -