Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche

0
18

Shugaban sashen yada labaran soji, Manjo Janar John Enenche ya ce yanzu Boko Haram bata da iko da kowanne gari a fadin kasar nan, musamman a arewa maso kudancin kasar inda yan ta’addan suka fi karfi.

Da ya ke magana a shirin gidan talabijin na Channels a wani shiri ‘siyasa a yau’, a ranar juma’a, Enenche ya yi bayanin cewa yanzu abun da ya rage a kasar shi ne ragowar marasa karfin abokan gaba (Boko Haram da mayakan ISWAP).

Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala’i har yanzu a Najeriya

“Suna guduwa daga jeji zuwa kogo daga kogo zuwa jeji kuma yanzu basu da iko akan ko wane a arewa maso gabas da ketare, a Najeriya” a cewar sa.

Bayanan na zuwa ne rana daya da ranar bikin tunawa da yan mazan jiya, don tunawa da jaruman soji da suka rasu.

Yayin da kasar ke ci gaba da samun nasara a yaki da yan ta’adda, wasu da dama na ci gaba da ganin laifin gwamnati a wajen nasarar yakin, cika har da wasu manyan jami’an gwamnati.

Duk da haka, gwamnati na ikirarin cewa ana samun nasara fiye da gwamnatocin baya.

Janar Enenche ya sake jaddada wannan ikirari ranar Juma’a, ya na nuna cewa “sojojin Najeriya solar iyakacin kokarin su shekarar da ta gabata wajen tabbatar da tsaro a kasar.”

“A 2015 kafin zuwan wannan gwamnati, akalla kananan hukumomi 170-20 na karkashin ikon yan ta’adda….a 2016 aka kwato gaba daya zuwa kulawar gwamnati da ikon ta”, a cewar sa.

What's On Your Mind?