Bloomberg: Kasashen Duniya Na Neman Taimakon Sin Dangane Da Allurar COVID-19

- Advertisement -

Bloomberg: Kasashen Duniya Na Neman Taimakon Sin Dangane Da Allurar COVID-19

Daga CRI Hausa

Kafar yada labarai ta Bloomberg ta ruwaito a jiya cewa, kasashen da suke fuskantar karancin allurar rigakafin cutar COVID-19 na bayyana burinsu na neman taimakon kasar Sin, duk da cewa, Amurka na jaddada karfinta na samar da allurar.

Bloomberg ta bayyana cewa, Amurka da EU suna namijin kokarin tinkarar cutar dake kan ganiyarta a kasashensu, amma Sin ta cimma nasarar dakile ta a cikin gida. Ta kara da cewa Amurka tana iyakacin kokarin yiwa al’ummarta allurar, inda ake zargin ta mallaki adadin allurar mai tarin yawa, matakin da ya rage burin sauran kasashe na neman taimakonta. (Amina Xu)

 

 

 

- Advertisement -