Bilkisu: Yarinya Mai Boyayyen Sirri A Cikin Shirin SIRRIN BOYE

0
119

Bilkisu: Yarinya Mai Boyayyen Sirri A Cikin Shirin SIRRIN BOYE

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Sunanta Bilkisu Salisu ‘yar kimanin shekaru 11 a duniya, wacce ta fito a matsayin Amira a cikin shirin talabijin mai dogon zango wato ‘SIRRIN BOYE’ kusan manyan jaruman Kannywood na cikin wannan shiri amma ita ce kashin bayan labarin, inda ta fito a matsayin wata hatsabibiya da idan ta kalli mutum zai kasance ko za a kashe shi ko kuma zai kashe wani. Kafin iyayenta da kuma jami’an tsaro su gano bakin zaren rayuka da dama solar salwanta, an kuma shiga bin bokaye da malamai domin warkar da ita daga kamun bakaken aljanu kamar yadda aka yi zargi daga farko. Jami’an tsaro masu kaifin basira da iya bin diddigi solar shiga matsanancin rudani a yayin nemo hanyar bayar da kariya ga wadanda ta kalla don ceto su daga halaka. Labari ne mai matukar sarkakkiya da tayar da hankali da fasihin marubuci Ibrahim Birniwa ya kirkira tare da rubutawa gami da hadakar zakakuran matasan marubutan Kannywood.
Ko yaya za a samo sabuwar jaruma mai karancin shekaru da zata iya hawa wannan matsayi na hatsabibiyar yarinya? Mai shirywa Maje El-Hajeej Hotoro ya shiga shawagin neman wannan yarinya wacce samunta na da matukar wahala musamman domin ba kowane iyaye ne zasu kyale ‘ya’yansu masu karancin shekaru shiga fim ba, kamar yadda ba kowacce yarinya ce zata iya samar da abinda ake so ba bayan bata taba yin fim ba. A karshe an samu Bilkisu a dalilin wata jaruma Nafisat Salisu wacce take jan fim mai dogon zango ‘MACEN SIRRI’ inda ta gabatar da kanwarta uwa daya uba daya domin gwada sa’arta, wanda nan take a wajen gwaji ta samar da abinda ake so.
Bayan tara manyan jaruman Kannywood Amira ta dake kamar wata tsohuwar jaruma ta ja wannan babban fim, shin ko yaya ta ji kafin kaukar wannan fim da kuma bayan daukarsa? “A’a ban taba yin fim ba sai akan Sirrin boye wanda kamfanin Sirrinsu Media suka shirya?
MOBILIZED9JA A YAU: Mai karatu zai so ya ji sunan ki da tarihin ki?
BILKISU SALISU: sunana Bilkisu Salisu, Amira kuma a cikin Fim ɗin Sirrin Ɓoye, an haife ni a watan Maris a shekarar 2010 a ƙaramar hukumar Tarauni dake jihar Kano, a unguwar Hotoro Ɗanmarke, na kuma fara makarantar Firamare a Edcellent worldwide Faculty duk a Hotoro, har yanzu ban gama ba ina can.
MOBILIZED9JA A YAU: Ya akai kika shiga masana’antar Kannywood?
BILKISU SALISU: na shigane ta hanyar yayata, lokacin da aka ce a kawo ni nayi fim, wanda kafin ma na fara sai da aka yi mani gwaji wato ‘Audition’ sai aka ga na dace kuma zan iya.
MOBILIZED9JA A YAU: Ya ki ka ji ranar farko da aka fara sa miki kyamara?
BILKISU SALISU: Kai tab naji tsoro gaskiya domin kuwa gani nayi ma kamar bazan iya ba amma daga baya da aka fara sai naji tsoron ya gudu, sannan nayi murna sosai fa naji dadi a raina kamar ba ni ba.
MOBILIZED9JA A YAU: Bayan fara dora miki kyamara wanne abu ne yafi burge ki a cikin Fim din?
BILKISU SALISU: wurin da ya burge ni suna da yawa amma inda akaje gurin Malam aka harbi malamin sannan aka dakk oni akayi gudu, nanne ya fi burge ni gaskiya don idan na tuno haka a raina sai inji dadi, sai kuma gurin da aka kai ni makaranta na kalli wani yaro na yanke jiki na fadi to nan ma yana burge ni sosai fa.
MOBILIZED9JA A YAU: bayan wannan Fim din naki na farko kina so ki cigaba da fitowa a fina-finai?
BILKISU SALISU: Ina so da gaske sosai.
MOBILIZED9JA A YAU: Duba da cewa wannan fim din kin fito kamar wata mayya wanda idan kika kalli mutum sai ya mutu ko wani abu mummuna zai similar shi, ba kya ganin idan Fim din ya fito mutane za su rika daukarki kamar wata mayya?
BILKISU SALISU: Ni bana wannan tsoron saboda na san cewa wannan Fim ne kuma kowa ma ya san fim ne.
MOBILIZED9JA A YAU: Ba kya ganin yin Fim zai iya tsayar miki da karatun ki?
BILKISU SALISU: Bana tsammanin fim zai iya tsayar dani, saboda ina karatu ina yin Fim ɗin, don ko lokacin da muke zuwa lokashon sai mun tashi daga makaranta sannan sai mu tafi wajen ɗaukar fim ɗin, kaga kuwa ba yadda za a yi fim ya hana ni yin makaranta ko kuma ya kawo min cikas a karatuna.
MOBILIZED9JA A YAU: ko me iyayenki suka ce lokacin da za ki fara Fim?
BILKISU SALISU: lokacin da Oga Maje El-Hajeej Hotoro ya kira maman mu ya gaya mata kawai sa tace ba damuwa, sannan ni kuma tace min inje Allah Ya bada sa’a in dage nayi ƙoƙari.
MOBILIZED9JA A YAU: A ƙarshe wanda kira zakiyiwa jama’a ko kuma yara ‘yan uwaki?
BILKISU SALISU: ina gaida kowa da kowa musamman Mamana da Babana, sannan ina yiwa Ogana Maje El-Hajeej Hotoro fatan alkairi, ina kuma kira ga ‘yan uwana yara da mu dage muyi karatu saboda sai da shine zaka iya yin komai musamman ta wajen cimma burin sa, mu dai na wasa mu kuma bi iyayenmu sau da ƙafa saboda malaman Islamiyyar mu suna cewa duk wanda ya bi iyaye kullum zai dinga samun nasara a rayuwa.
An tambayi Nafisat Salisu a matsayinta na yaya ga wannan jaruma mai tasowa sai ta ce;
NAFISAT SALISU: Kusan zance ni taimnako na ma aka yi kuma naji daɗi sosai, kamar yadda na bayyana a kwanakin baya na sha wahala sosai lokacin da zan shiga Kannywood, to kaga da ƙanwata ta nuna tana son wannan abun ba zan so ta sha wahalar da ni na sha ba, gashi kuma ta samu abun cikin sauƙi, maganar gaskiya naji daɗi.
Fim din ya zo da sabon salon labari mai jan hankali gami da rudani, wanda a masana’antar Kannywood ba a taba samar da irinsa ba, kamar yadda aka yi kokarin samar da kayan aiki na zamani masu nagarta gami da kwararrun ma’aikata. Abin jira a gani shine ko yaya ‘yan kallo zasu karbi wannan hatsabibiyar jaruma? Shakka babu lokaci ne zai tabbatar da hakan.

 

What's On Your Mind?