Bikin Sallah: Sai Da Zaman Lafiya Al’umma Za Ta Cigaba: Inji Sarkin Lokoja

- Advertisement -

Bikin Sallah: Sai Da Zaman Lafiya Al’umma Za Ta Cigaba: Inji Sarkin Lokoja

Daga Ahmed Muhammed Danasabe,

An bayyana zaman lafiya a matsayin ginshiki da kuma kashin bayan ci gaban kowace al’umma.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji( Dr) Muhammadu Kabir Maikarfi Na 111, a sa,ilin da yake yiwa jama’ar masarautarsa jawabin goron sallah a fadarsa, kadan bayan an sauko daga sallar Idi, a jiya alhamis.

Alhaji Kabir Maikarfi, wanda yace rashin zaman lafiya na matukar gurgunta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da kuma siyasa, ya kuma bukaci jama’a dasu zauna lafiya da juna.

Mai martaba Sarkin ya kuma yi kira ga matasa dasu guji aikata laifufuka da suka hada da ta’addanci da satar jama’a da tu’ammali da miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin asiri da dai makamantarsu

Alhaji Kabir Maikarfi har ila yau ya shawarci matasa dasu rungumi sana’oin hannu domin maganin zaman kashe wando.

Sarkin wanda har ila yau,ya nananta muhimmancin neman ilimi, ya kuma yi kira ga matasan dasu nemi ilimi domin ganin solar bada gudunmwarsu ga ci gaban al’umma dama kasa baki daya.

Daga yake taya al’ummar masarautarsa murnan kammala Azumin watan Ramadana kuwa, Alhaji Kabir Maikarfi ya kuma bukace da su yi aiki da darassan da suka koya a cikin watan mai tsarki.

Daga bisani, ya yi wa jihar Kogi da kuma kasa addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya, musamman a wannan lokaci da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro.

A karshe Sarkin na Lokoja, ya taya al’ummar masarautarsa murnan bukukuwan karamar sallar.

 

- Advertisement -