Bikin Ranar ‘Yan Jarida: Ku Yi Amfani Da ‘Yancinku Cikin Kwarewa, Buhari Ya Shawarce Su

0
78

Bikin Ranar ‘Yan Jarida:  Ku Yi Amfani Da ‘Yancinku Cikin Kwarewa, Buhari Ya Shawarce Su

Daga Mahdi M. Muhammad,

Da yake ana bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, da aka saba gudanarwa a duk ranar three ga watan Mayu, Shugaba Muhammadu Buhar, ya bayyana kudurinsa na ci gaba da bayar da goyon bayan ga ‘yancin aikin jarida duk da cewa ya bukaci kwararrun kafafan yada labarai da su yi amfani da ‘yancin cikin kwarewa, kuma ta yadda ya dace.

 

Yayin da yake murnar wannan rana ta musamman tare da manema labarai, shugaban a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa, ‘yancin ‘yan jarida ba shi da iyaka a cikin dimokiradiyya da za ta bunkasa, yana mai cewa, dole ne a yi amfani da ‘yanci yadda ya kamata.

 

“Cewa komai ya halatta ba yana nufin cewa babu wasu ka’idoji na daidaito ba ne, musamman a tsarin siyasa da ake fuskantar kalubale kamar namu yanzu. Dole ne kafafen yada labarai su kasance masu lura da halin da muke ciki a matsayinmu na kasa, kuma duk wani abu da zai kara dagula lamura, da kara rura wutar rikici, ya kamata a kauce masa. Kafofin yada labarai na bukatar tabbatar da cewa yayin da suke fadakarwa, ilimantarwa, nishadantarwa da kuma sanya jadawalin tattaunawa ga jama’a, hakan ba ya karfafa kalamai da ayyukan da za su iya harzuka hadin kanmu a cikin bambanci,” in ji Buhari.

 

‘Yancin lasisi, Shugaban ya ce, ya bambanta da ‘yanci tare da alhaki, kuma ya zargi kafafen yada labaran Nijeriya da su rungumi na baya, maimakon na da.

 

A bangaren gwamnati, Shugaba Buhari ya yi alkawarin kara hadin gwiwa da kafafen yada labarai domin sauke nauyin da ke kan su, daidai da taken ranar ‘yancin ‘yan Jaridu ta duniya a wannan shekarar.

 

Don haka, ya umarci wadanda ke gudanar da bayanai don gwamnati da su yi komai don amfanin jama’a, sannan kuma ya karfafa wa kafafen yada labarai su yi amfani da dokar ‘yancin ba da bayani (FoIA) don samar da ayyukansu cikin sauki.

 

Shugaban ya gabatar da cewa yana da matukar muhimmanci samun damar samun ingantattun bayanai a zamanin da ake samun bata gari, yada labarai da kuma kalaman nuna kiyayya, duk suna haifar da fitina a cikin al’umma.

What's On Your Mind?