Bikin Cikar NAF Shekara 57: Buhari Ya Kaddamar Da Jirgin Yaki Samfurin JF-17 Guda 3

- Advertisement -

Bikin Cikar NAF Shekara 57: Buhari Ya Kaddamar Da Jirgin Yaki Samfurin JF-17 Guda 3

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Shugaba Mohammadu Buhari ya sanya sabbin jiragen yaki guda uku samfurin ‘JF-17 Thunder Multi-role’ a cikin kayan yakin rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) don bunkasa ayyukanta.

Da yake gabatar da bikin a ranar Alhamis a Makurdi yayin bikin karshe na NAF 57, Buhari ya ce, hukumar ta cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya ba ta na kare martabar yankin kasar.

“A wannan lokacin, na shigar da jirgin sama na JF-17 Thunder cikin aikin rundunar Sojin saman Nijeriya da kuma kasar mu kamar NAF 720, 721 da 722. Yayin da kuke tuka wadannan jirage, ina yi muku fatan gudanar da ayyukan tashi lafiya a matsayin sakamako mai tasiri,” in ji shi.

Buhari, wanda Ministan tsaro ya wakilta, Manjo-Janar mai ritaya Bashir Magashi, ya ce, jiragen saman uku za su bunkasa ayyukan hukumar tare da kara ingancin yaki da ta’addanci, tayar da kayar baya, ‘yan bindiga da sauran nau’ikan laifuka.
Ya kara da cewa, shigar da jirgin wani mataki ne na cika daya daga cikin alkawuran da ya dauka a farkon gwamnatinsa, wanda shi ne inganta ababen extra rayuwa da kayan aikin sojoji.

“Hakika ya dace da cewa ana nuna karshen babban bikin na wannan shekara tare da shigar da sabbin jiragen yaki guda uku JF-17 Thunder masu fada-a-ji a cikin kayan rundunar Sojin saman Nijeriya.

Wannan bikin karramawar na da matukar muhimmanci a wurina saboda yana nuna wani mataki na cika daya daga cikin alkawuran da na dauka a farkon gwamnatina, don inganta kayayyakin aiki da kayan aiki na Sojojin da sauran hukumomin tsaro don yaki ta’addanci, kwarewa da isar da ayyukansu,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “jirgin saman yaki mai saukar ungulu na 3 JF-17 Thunder wanda ake karawa a cikin kayan rundunar sojin sama ta Nijeriya a yau ba shakka zai bunkasa karfin aikin hukumar. Kuma a kara kaimi wajen yaki da ta’addanci, tayar da kayar baya, ‘yan bindiga da sauran nau’ikan aikata laifuka a kasar.”

Buhari ya ce NAF, tun lokacin da aka kafa ta a 1964, ta taka muhimmiyar rawa a cikin tsaron kasa da kuma ayyukan kiyaye zaman lafiya a Nahiyar Afirka.
Ya kuma yaba wa hukumar kan irin rawar da ta taka a ayyukan da ake yi na magance masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas da kuma ayyukan yaki da ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da kuma sauran ayyukan a sauran sassan kasar.

Ya kuma yaba wa ‘yan Nijeriya wadanda suka ci gaba da nuna adawa ga duk wasu maganganun batanci da wasu tsirarun mutane ke yi na raba kasar da haifar da rashin jituwa a tsakaninsu.

“Dole ne kuma in jinjina wa juriyar mutanen Nijeriya wadanda suka ci gaba da yin tirjiya da duk wasu munanan abubuwa da ke neman raba mu da maganganunsu na lalata da farfaganda ta rashin gaskiya. Ina son yin amfani da wannan damar don karfafawa dukkan ‘yan kasa masu bin doka da oda su ci gaba da tsayawa tare, ba tare da la’akari da kabila, addini ko siyasa ba, don neman babban burin samar da kasa mai cikakken tsaro, hadin kai da ci gaba a gare mu da kuma tsararrakinmu wadanda ba a haifa ba, tunda ba mu da wata hanyar da ta wuce wannan,” in ji shi.
Buhari ya kara godiya da goyon bayan da Gwamnatin Pakistan ke bayarwa musamman kokarin Jakadan Pakistan a Nijeriya na dorewar kawancen da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, kasashen biyu za su ci gaba da daukar matakan da za su kara dankon alakar da ke tsakanin su don ci gaban ‘yan kasar ta.

“Wannan gwamnatin za ta ci gaba da aiki tare da abokan huldar mu da sauran mambobin kasashen duniya domin samar da hanyoyin magance matsalolin kalubalen ta’addanci da yaduwar kananan makamai,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Lallai, irin wannan mu’amala mai amfani da juna wani bangare ne na sadaukar da kanmu ga dukkan al’umma da tsarin bil’adama don magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya, Afirka ta Yamma da kuma dukkan nahiyar Afirka.”
Tun da farko, a nasa jawabin, Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya ce, NAF ta shigar da jimillar jiragen sama 26 tsakanin shekarar 2015 zuwa yau, ciki har da sabbin jirage uku da aka shigo da su.

Amao ya kuma bayyana cewa aikin na sa ran karin jiragen sama 20 zuwa cikin kasar daga watan Yulin wannan shekarar.
Ya bayyana cewa, jiragen da ake tsammani solar kasance jiragen 12 ‘A-29 Tremendous Tucano’ daga Amurka da kuma Jirgin Sama mara matuka (UAb) guda takwas.

“Bari in sanya a rubuce cewa a karkashin Gwamnatin mai ci yanzu, Sojojin Saman Nijeriya solar shigo da sabbin jiragen sama da 23 daga shekarar 2018 har zuwa yau, wadanda suka hada da jirgin ‘Mushshak coach plane’ 10 da kuma jirgin ‘rotary wing fight platforms’ guda 13,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Fagen yakin solar hada da jiragen yaki masu saukar ungulu na MI-35M, jirage masu saukar ungulu na ‘Agusta 109 Energy helicopter’ guda 2 da kuma Mi-171E four da Belt 412 guda 2.

- Advertisement -