Bidiyona Ina Karbar Dala, Shiri Ne Kawai, Inji Ganduje

- Advertisement -

Bidiyona Ina Karbar Dala, Shiri Ne Kawai, Inji Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya musanta bidiyon zarginsa da karbar rashawar Dala daga hannun wani dan kwangila a Jiharsa.

Ganduje ya ce saddabaru aka yi wa bidiyon da aka baza, shekara uku da suka wuce, inda a ciki aka gan shi yana karbar bandur-bandur na dala yana cusawa a cikin aljihunsa.
“Tabbas bidiyon bogi ne kuma muna kan bincike da wasu tsare-tsare ta karkashin kasa da ba za mu bayyana ba. Amma tabbas suddabaru aka yi wa bidiyon don a goga mana kashin kaji,” inji Ganduje.

Tirkashi Ganduje yayi Martani Mai zafi akan yimin akan Bidiyon karba Dalla

Ya fadi haka ne bayan wani dan asalin Jihar Kano, kuma mai fafutka, Kabiru Sa’idu Dakata, ya tambaye shi kan yaki da gwamnatinsa ke yi da cin hanci da kuma inda aka kwana wajen binciko gaskiyar bidiyon dalar.

Kabiru Dakata ya yi tambayar ce a lokacin shirin da aka yi da gwamnan a Sashen Hausa na BBC, mai suna ‘A Fada A Cika’ da ke bibiyar alkawuran zabe da ayyukan gwamnoni.

Ya ce an kirkiri bidiyon dalan ne domin a bata masa suna don hana shi tsayawa takara, amma wadanda suka yi shi za su fuskanci hukunci.

“Tsagwaron karya ce saboda babu abin da ya faru. Makarkashiya ce aka shirya domin a hana ni tsayawa takara da cin zabe, amma na yi takarar kuma na lashe zaben. Amma wanna ba shi ne abun damuwa ba, babban abin shi ne za mu yi maganin.”

- Advertisement -