Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa ‘yan bindiga a Katsina

0
44
  • Dakarun sojin saman Operation Hadarin Daji solar ragargaza ‘yan bindigar daji

  • Hakan ta faru bayan samamen da sojin suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu

  • Maboyar ‘yan ta’addan tare da wasu masu tarin yawa daga cikinsu solar halaka

Rundunar dakarun sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta halaka ‘yan bindiga masu tarin yawa da ke yammacin Wagini ta jihar Katsina.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar, ta samu nasarar ragargaza sansanin wasu ‘yan bindiga ne bayan bayanan sirrin da suka samu na wanzuwar wasu ‘yan bindiga.

Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Asabar.

Enenche ya ce solar aiwatar da samamen ne a ranar 8 ga watan Oktoba bayan bayanan sirri da suka samu wanda kuma suka tabbatar ta jiragen yaki.

A hakan aka hango ‘yan bindiga tare da daruruwan shanu a sansaninsu.

Bidiyo: Rarara Ya Saki Sakamakon Gasar wakar Dogara Ya Dawo

Ya ce jiragen yakin solar ragargaji wurin inda suka tarwatsa sansanin tare da kashe da yawa daga cikin ‘yan bindigar.

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba ya ce Najeriya tana da miliyoyin mutane da ke fama da matsanancin talauci.

Ya fadi hakan yayin da yake jawabi a wani taro a fadar shugaban kasa Abuja. Ya ce shugabannin da aka zaba basu da amfani indai har basu hada karfi da karfe wurin taimako a kan matsalar nan ba.

Ya ce, “Dole ne kowanne shugaba ya fahimci yadda zai tafiyar da mulkinsa. Idan aka kalli halin da miliyoyin talakawan Najeriya suke ciki, gashi yanzu cutar COVID-19 ta kara dagula komai, talauci da rashin aikin yi solar yawaita.”

What's On Your Mind?