Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da ‘ya’yanta

0
103

Hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya’yanta tun yarinta har girmansu. Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai.

Bidiyon wata mata mai sana’ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana’arta goye da jaririnta.

A bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti.

Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta

Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Fb, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Ta wallafa bidiyon inda har tayi wani dan tsokaci akai, ta kuranta kanta, tace hakika abubuwan arziki basu biyo mutum, sai ya mike, ya dage kuma ya zage wurin nema da kansa.

Yayin da mutane da dama suka yi ta yaba mata akan namijin kokarin da tayi, wasu kuma solar ce tasa rayuwar jaririnta a cikin hatsari.

Gaskiyar dalilin da ya sa wata mata ƴar Kano ta kashe ƴaƴanta 2

Ta mayar da martanin masu cewa tasa rayuwar jaririnta a hatsari, inda ta ce ta goya jaririnta ne yayin da zata dauki hoton don nuna wa duniya irin jajircewarta a matsayinta na uwa.

A tsokacin da tayi tace, “hakika duk wata nasara bata biyo mutum inda yake, sai ya fita ya nema.

Dangane da jaririna, kada ku damu, nayi bidiyonne don in nuna muku ni uwa ce. Ban taba aiki da jaririna a baya na ba.

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Oluwafunlola, ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, yadda saurayinta ya yaudare ta.

Budurwar ta bada labarin yadda ta gano cewa saurayin da ta ke kauna yana da wata budurwa daban.

Ba wannan kadai ne yafi daga mata hankali ba, hankalinta ya tashi ne a lokacin da ta gano ashe amfaninta daya ne a wurin sa, wato girki. Kuma ko girkin, ba shi kadai ne take yi wa ba, har da dayar budurwarsa.

A yadda budurwar ta bada labari, tana tura wa saurayin nata abinci ne ta masu babur din haya. Idan dayar budurwar ta tambayi saurayin, sai ya ce ai dama aikawa yake yi ana siya mishi.

 

Courage et détermination 🤛,le bonheur ne vient pas frappé à la porte, on le cherche.pour l’enfant ne vous inquiétez pas c’était pour juste faire la vidéo pour montrer que je suis mère sinon je travaille jamais avec l’enfant. Je travaille jamais sans combinaison

Posted by Sognan Silla on Friday, September 11, 2020

What's On Your Mind?