Bidiyon Da Wasu Matasa Nayiwa wata Mai Abaya Yasan Mansurah Isah Da Fauziyya D Suleman Martani mai Zafi

- Advertisement -

Yan kwanakin nan anka ga wani bidiyo yana yawo ya harzuka Mansurah Isah da Fauziyya d Suleman sunyi maganganu sosai akan wannan abun da matasa nayiwa wannan yarinya inda Fauziyya d Suleman ke cewa.

“Wannan shine abun da masu ilimi su ka yi na wulakanta diyar wani, kanwar wani Yayar wani, wai wadannan daliban university ne na Wudil, to don Allah idan masu ilimi za su wannan sakarcin me ka ke tunanin jahilai za su yi?
Shigar da yarinyar nan ta yi babu inda ya kama jikinta, wayo gwara mace ta saka matsatsun kaya kenan, abun ya wuce hankali, wannan tsagwaron rashin tarbiyya ne.”

Wanda itama Mansurah Isah tayi nata kamar haka.

Yanzu Shigar Mutunci ya zama abin wulakanci?? To some yan samari, da kananan yara maza a waje, Yanzu kuna ganin kunyi daidai da sabon salon nan ?

Yarinya ta saka daya daga cikin kayan mutunci da muke alfahari dashi, Amma kuna wulakanta ta kuna cin zarafin ta akan hanya !

So kuke su fito tsirara? So kuke ta saka wando ? Kodai alamomin karshen duniya ne wannan ? Abin yana bani tsoro sosai. Mai kuke so ne ? Yanzu a matsayin ku na masu kaunar Manzo SAW, kuna cin ZARAFIN mace da shigar mutuncin ta. Sai yaran mu sun daina saka Abaya sun dawo saka mini skirt da Wanda sannan zakiyi alfahari ko zaku samu nutsuwa ??

Wallah ba kyau, wallah shaidan yana samun Nasara akan ku.”

https://www.instagram.com/_u/mansurah_isah/?utm_source=ig_embed&ig_rid=13345854-e41a-4dab-b6d4-385705a03ac8&ig_mid=CD10A5FE-F5D3-46AD-BC4E-36A714F4824F

- Advertisement -