Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

0
10

Wani bidiyo ya shahara a shafin soshiyal midiya na wasu da ake zaton yan damfara ne suna watsa bandir din kudi a kogi.

Yan Najeriya a shafin soshiyal midiya na ganin cewa abunda suka aikata asiri ne da nufin bunkasa arzikinsu.

A bidiyon, an gano mazan su hudu suna wanke fuskokinsu a cikin ruwan kazanta.

Yan Najeriya solar je shashin sharhi na bidiyon wanda @lindaikejiblogofficial ta wallafa a Instagram.

Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

@officialbecks ta ce:

“Suna biyan shaidan bashin abunda yake nashi.”

@iamvictoria_richard ta ce:

“Idan arzikinka ba na Allah bane, shaidan zai ta wahalar da kai a koda yaushe.”

@angelsvirginhair_ ta rubuta:

Sojoji sun hallaka yan ta’addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7

“Ta Yaya hakan ya zama asiri?? Allah ya kyauta. Kamar yadda kuka yarda da Annabi Isah sannan kuke zuwa coci da sadaka, sauran ma suna da nasu al’adan da suke ba abun bautar su. Wannan ba tsafi bane.”

 249 total views,  3 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here