Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

0
104

Wani bidiyon amaryar da ta tsere ranar aurenta bayan ta gano saurayin da zata aura yana tarayya da kawarta ya karade kafafen sada zumunta. Al’amarin ya faru ne a Space 2, a Garki jihar Abuja.

Kamar yadda aka wallafa a shafin sada zumunta, wata mata na cikin mota zata nufi wurin daurin aurenta, kwatsam sai aka kirata a waya.

Inda aka sanar da ita cewa saurayin da zata aura yana lalata da kawarta ana saura kwanaki kadan a daura aurensu. Take anan amaryar ta dakatar da motar, ta tsere.

Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

Kalli Videon Yadda Jami’an Tsaro suka kame masu satar mutane da suka dade suna nema

Bidiyon ya bayyana yadda kawayenta suka biyo bayanta don gudun kada taje ta salwantar da rayuwar ta.

Amaryar tayi ta kuka tamkar zata kashe kanta, inda kawayenta keta kokarin rarrashin ta.

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode, yayi magana akan bidiyon da ya bayyana yana dukan matarsa, Treasured Chikwendu.

Tsohon ministan yayi magana ranar Asabar akan bidiyon da yayi ta yawo a duniya wanda aka ganshi yana dukan matarsa, inda yace ya kama ta da namiji a gadonsu na sunna ne.

Fani-Kayode yayi maganar ranar Lahadi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Fb akan al’amarin. Ya ce ya boye haukar matarsa na tsawon shekaru 7 ba tare da ya bayyanawa duniya ba.

 

Posted by Fasanmi Paul Abiola on Monday, 5 October 2020

What's On Your Mind?