Bidiyo : Ana iya sitta Shawwal a kowanne wata- Sheikh Umar Sani Fagge

- Advertisement -

Malamin addinin musulunci nan a nan Kano Sheikh Umar Sani Fagge ya ce ana iya azumtar sitta Shawwal a kowanne wata ba sai a Shawwal ba.

Kano Focus ta ruwaito malamin na wannan bayani ne cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumuta na zamani.

Ya ce azumtar sitta shawwal cikin watan Zul-hijja ma ya fi lada ga wanda zai yi.

Ya c Annabi SAW ya ambaci yin azumin ne a cikin watan shawwal dan saukakawa ba dan kebancewa ba.

Ya ce wanda duk ya azumci watan Ramadan ya kuma yi wani azumin guda shida kafin Ramadan ya zagayo to dai-dai ya ke da ya azumci shekara.

Jahilai ke sukar Fatawar Dr Bashir kan sakin aure a film-Sheikh Umar Sani Fagge

EFCC ta gurfanar da Jami’in Hukumar Gyaran Hali gaban kuliya

“Abinda nakeso da farko, Annabi SAW cewa ya yi man sama Ramadan wa atba’ahu sittan min shawwal fa-ka-anna-ma samaddahara.

“To sittan min Shawwal wannan nakeso mu fahinta, me yasa Annabi SAW ya fadi Shawwal, littakfifi la littakhsis, dan saukakawa ba dan kebancewa ba.

“Wanda duk ya yi Ramadan a bayansa kafin wani Ramadan din yazo indai ya yi zumi shida to ka annana samaddahara.

“Yafadi Ramadan ne littakhfifi saboda baka dade da rabuwa da azumi ba, in kazo ka yi shi baka riga ka saki jikiba baka riga ka sangarta ba ya fi maka sauki shi yasa ya fadi sitta.” A cewarsa.

Ga mai buƙata saurare daga bakin malamin ga faifan bidiyon nan sai ku saurara kuji.

- Advertisement -