Bayern Munchen Ta Dauki Sabon Mai Koyarwa

0
74

Bayern Munchen Ta Dauki Sabon Mai Koyarwa

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, Julian Nagelsmann ya amince zai koma horar da kungitar Bayern Munich daga kakar wasa ta badi zuwa kakar wasa biyar, kamar yadda kungiyar ta Jamus ta sanar.

Wanda ke jan ragamar kungiyar a yanzu haka shi ne mai koyarwa Hansi Flick ya sanar cewar zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana domin ya karbi ragamar koyar da tawagar ‘yan wasan kasar Jamus.

Julian Nagelsmann, mai shekara 33 a duniya, daya ne daga cikin fitattun matasan kociyoyin da ake ji da su a Turai a yanzu, wanda ya kai kungiyar RB Leipzig wasan dab da wasan karshe a Champions League a bara.

Kocin dan kasar Jamus wanda zai karbi jan ragamar kungiyar ta Bayern Munich daga ranar daya ga Yulin bana, zai sa Bayern ta biya rarar kudi da ya kai fam miliyan 20 ga kungiyar RB Leipzig.

Sannan Nagelsmann ya zama matashin mai horar da wasa a tarihin Bundesliga mai shekara 28 a lokacin da ya ja ragamar Hoffenheim a watan Fabrairun shekara ta 2016 kafin ya koma RB Leipzig.

Bayan da ya koma kungiyar Leipzig ne a shekarar 2019 ya kai kungiyar mataki na uku a gasar Bundesliga da karawar dab da karshe a kofin zakaru na Champins League a kakarsa ta farko.

Bugu da kari, kungiyar Leipzig tana mataki na biyu a gasar Bundesliga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Wolfsburg ta uku kuma saura karawa uku-uku a karkare gasar Jamus ta bana.

What's On Your Mind?