Bayelsa: APC Ta Kaddamar Da Kwamitin Sulhu Kan Zaben Cike Gurbin Sanatoci

0
45

APC Ta Kaddamar Da Kwamitin Sulhu Kan Zaben Cike Gurbin Sanatoci

A shekaran jiya ne jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamitin sulhu da sasantawa kan zaben cike gurbi na mazabun ‘yan majalisun Dattibai na Bayelsa ta Yamma da ta Tsakiya, inda APC din ta nada Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin shugaban kwamitin mai mutum 11.

Shugaban kwanitin rikon kwarya da shirya babban taron jam’iyyar, kuma Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ya kaddamar da kwamitin a sakatariyar jam’iyyar ta APC da ke Abuja.

Bayelsa: APC Ta Kaddamar Da Kwamitin Sulhu Kan Zaben Cike Gurbin Sanatoci

Buni wanda ya samu wakilcin sakataren kwamitin rikon kwaryan Sanata John James Akpanugedehe, ya bukaci mambobin kwamitin su yi amfani da dimbin basira da tasirinsu wajen samar da nagartacciyar fahimtar juna don kowane dan jam’iyyar ya ji ana damawa da shi, su kuma kimtsa da jajircewa wajen ganin jam’iyyar ta lashe zaben na Sanatocin Bayelsa ta Tsakiya da ta Yamma don samun karin goyon baya a majalisar tarayya.

A wata sanarwar manema labarai da ya fitar Ismaila Uba Misili, babban mai taimaka wa gwamnan jihar Gombe kan hulda da ‘yan jarida ya ce gwamnan ya amshi mukamin da aka nada shi hannu biyu-biyu tare da shan alwashin yin aiyukan da za su kai ga kyautata jam’iyyar domin ganin ta samu gagarumar nasara a yayin zaben.

Gwamna Inuwa Yahaya ya baiwa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta APC tabbacin cewa za su yi dukkannin mai yiwuwa na ganin photo voltaic sauke nauyin da aka dora musu.

Ya ce matsalolin da jam’iyyar ta APC ta shiga photo voltaic janyo mata faduwa a zabuka da dama ciki har da Jihar Zamfara da Bayelsa da kuma jiha ta baya-bayan nan Jihar Edo.

Wadanda Suka Sace Tsohon Kwamishinan Nasarawa Na Neman Miliyan N30

Ya ce wadannan faduwa zaden abun takaici ne, ya na mai cewa jam’iyyar da dauki darasi, darasin da zai karfafa gwiwan ‘ya’yanta su kara dunkulewa tare da samar da damammakin sasantawa ta hanyar cude ni in cude ka.

Ya ce manufar ‘ya’yan jam’iyyar daya ne, wanda kuma shi ya kaita ga cin nasara tun 2015, yana mai cewa “Siyasa batu ne na tafiyar da kyakkyawar alaka da jama’a da ke da muradi iri guda.”

Gwamna Inuwa ya ce yayin da jam’iyyar ke kokarin hidimtawa ‘yan Nijeriya, akawai bukatar ta kara kokari don karfafa ikonta a matakin kasa da na jihohi.

“Ina kira ga mambobin kwamitin gudanarwan jam’iyyarmu na kasa da shugabannin jam’iyyar na Jihar ta Bayelsa, su lalubo manyan matsalolin da ke addabar jam’iyyar don mu samu damar magance su.”

Ya ce jihohi da dama photo voltaic dinke barakar su, lamarin da ya sa manyan kusoshin da suka fice a cikinta suka sake komawa.

Gwamnan na Gombe sai ya mika godiya ga kwamitin gudanarwan jam’iyyar bisa ganin cancanta da nagartansu har ya zabo su don su bada tasu gudunmowa a wannan kwamiti, yana mai baiwa jam’iyyar tabbacin ba za su ba ta kunya ba.

Ya ce “Ba tare da nuna damuwa kan dimbin nauyin da ke kanmu ba, kowane da a wannan kwamitin yana sane da irin matsalolin da jam’iyyar ke fama da su, wanda hakan ya janyo kafa wannan kwamiti dake kula da harkokin jam’iyyar, don haka ba abin da za mu bari har sai mun ga munyi nasarar sauke nauyin da aka dora mana.”

Yayin wani taron manema labarai bayan kammala kaddamarwar, gwamnan ya jadada muhimmancin gina kwakkwarar jam’iyya dunkulalliya, yana mai yaba wa kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar karkarshin Gwamna Buni bisa kokarin da ya ke yi na cimma wannan kuduri.

A wata sanarwar manema labarai da jam’iyyar APC ta kasa ta fitar dauke da sanya hannun Yekini Nabena, mataimakin sakataren yada labaranta, ya nuna cewa mambobin kwamitin photo voltaic hada da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe a matsayin Shugaban kwamitin photo voltaic kan zaben cike gurbin ‘yan majalisun Bayelsa da zai gudana a ranar 31 ga watan Oktoba, yayin da kuma Sanata Obie Omo-Agege ya kasance mataimakin Shugaban.

Yekini ya nuna cewa mambobin kwamitin kuma photo voltaic hada da Sanata Abdullahi Sahabi, Sanata Ali Ndume, Sanata Uba Sani, Ambasada Fatima Goni, Sanata Chris Adegije, Alhaji Yusuf O. Ocholi, Chief Enyi O. Enyi da kuma Pearl Ekebong Inwang dukkaninsu mambobi, sai kuma Barista Ekemini Cletus Udoh ana nada a matsayin sakataren kwamitin.

What's On Your Mind?