Bayan shekaru biyar, an ceto daya daga cikin yan matan Chibok

0
18

Daya daga cikin dalibai matan sakandaren Chibok, Hauwa Halim Maiyanga, ta samu yanci bayan shekaru biyar da yan ta’addan Boko Haram suka kwasheta da kawayenta.

Hauwa na cikin matan makarantan sakandaren gwamnatin mata dake Chibok, jihar Borno, ranar 14 ga Afrilu, 2014.

A cewar TheCable, wata majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa inda aka ceto daruruwan mutanen da yan Boko Haram suka sace.

Bayan shekaru biyar, an ceto daya daga cikin yan matan Chibok

Rashida mai Sa’a tayi Kira ga Shugaban Buhari Kan sababbin Hafsoshin Tsaro Da Ya Nada

“Tsawon wata daya yanzu, Sojojin atisayen tura Takai bango da Lafiya Dole na ruwan wuta a dajin Sambisa da mabuyan Boko Haram, kuma an ceto mutane da yawa,” yace.

“Lokacin da aka kashe makiyan, an sake wadanda suka kama. Yar makarantan Chibok na daya daga cikin wadanda aka ceto, bayan da aka tarwatsa mabuyarsu. Akwai wasu mata da yawa, har yanzu muna kokarin gano inda aka sace su.”

Wani mazaunin Chibok wanda ya tabbatar da hakan ya ce an tuntubi iyayen yarinyar kuma ba da dadewa ba zasu tafi hedkwatan rundunar Operation Lafiya Dole dake barikin Maimalari, Maiduguri, birnin jihar Borno.

“Yanzu haka ana duba ta a asibitin Sojojin dake wajen,” majiyar ta bayyana.

A bangare guda, Abubakar Shekau, shugaban tsagi guda na kungiyar Boko Haram ya fitar da sabon sautin murya inda ya yi magana sport da nadin sabbin manyan hafsoshin Najeriya, inda ya ce babu wani abu da za su iya tabukawa da magabatansu ba su yi ba a yaki da ta’addanci a arewa maso gabas, HumAgle ta ruwaito.

A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, Shekau ya ce ya ji labarin yi wa tsaffin manyan hafsoshin tsaron murabus da maye gurbinsu da sabbi amma ya yi kira garesu su amshi musulunci.

What's On Your Mind?