Bayan dawowa daga Landan, hotuna sun nuna Buhari ya halarci zaman Tafsirin Al-Qur’ani

0
184

Bayan dawowarsa daga Landan inda ya tafi jinya, shugaba Muhammadu Buhari ya halarci zaman Tafsirin watan Ramadana a Masallacin fadar shugaban kasa, Aso Villa.

Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya halarci Tafisirin ne ranar Talata, 20 ga Afrilu, 2021.

A cikin hotunan da ya saki, an ga shugaban kasa tare da hadimansa na jiki zaune cikin Masallaci tare da baiwa juna tazara don kariya daga cutar Korona.

Ɗan Najeraya mai shekaru 23 ya zo na ɗaya a gasar Al-Qur’ani ta duniya a ƙasar Kenya

Daga cikin wadanda ke hallare akwai hadimi na Protocol, ADC, dss.

Kamar yadda aka saba, Masallatai a fadin Najeriya sun kaddamar da Tafsirin Al-qur’ani cikin watan Ramadana.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’advert, ya umurci daukacin al’ummar Musulmi su tashi da azumin watan Ramadana ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021.

Babban Malami, Shaykh Muhammad Bin Uthman, ya bayyana wasu fa’idoji 15 dake cikin wannan sabon wata da kuma ibadan da za’a gabatar a ciki.

What's On Your Mind?