Bayan ASUU, NASU da SSANU, malaman makarantun Poly zasu shiga yajin aiki

0
92
  • Da alamun daliban makarantun gaba da sakandare da da sauran hutu a gida bayan hutun cutar Korona

  • Yayinda malaman jami’o’i suka lashi takobin ba zasu koma aiki ba, na Poly na barazanan tafiya

  • Gwamnatin tarayya ta ce malaman su canza tunani su koma bakin aiki

Manyan ma’aikatan makarantun fasaha a Najeriya watau Poly solar yi barazanar shiga yajin aiki nan da makonni uku idan gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalolin da suke fuskanta sport da manhajar biya albashi ta IPPIS

Ma’aikatan karkashin kungiyar manyan ma’aikatan makarantun fasaha a Najeriya SSANIP, solar yi ganawar gaggawa a hedkwatar kungiyar kwadago ‘Labour Home’ dake birnin tarayya Abuja.

Solar bayyana rashin amincewarsu da yadda hukumar kula da makarantun fasaha na kasa NBTE ke gudanar da wasu ayyukanta.

Shugaban kungiyar, Philip Ogunsipe, ya bayyanawa manema labarai cewa akwai matsaloli daban-daban da suke fuskanta da manhajar IPPIS.

Bayan ASUU, NASU da SSANU, malaman makarantun Poly zasu shiga yajin aiki

Daga ciki akwai rashin samun mafi karancin albashi, zabge musu kudin da akeyi ba gaira ba dalili, rashin biyan ma’aikatan lafiya kudin hadarin COVID-19, bata lokaci wajen biyan alawus da kuma cire kudin harajin da ya saba hankali.

Ogunsipe yace: “Saboda haka, kungiyar na kira ga dukkan hukumomin gwamnati su gaggauta magance wadannan matsalolin da aka lissafo.”

“Hakazalika, kungiya na son sanar da cewa inda ba’a magance matsalar IPPIS ba cikin kwanaki 21 daga yau, za ta canza ra’ayinta kan manhajar.”

Wani saurayi ya saki bidiyon tsiraicin tsohuwar budurwarsa bayan da ya zarge ta da yin lalata da ita a wani otal da ke Sakkwato

Sport da matsalolin da suke fuskanta da hukumar kula da makarantun fasaha na kasa NBTE kuwa malaman solar ce “idan ba’a magance matsalolin nan da kwanaki 21 da wannan takarda ba, za’a shiga yajin aiki.”

A bangare guda, karamin ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya yi kira ga ‘yan kungiyar ASUU na malaman jami’a, su shiga harkar noma.

Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa ana bukatar karin manoma, don haka malaman makarantar na iya rabuwa da aji, su koma gona.

Ministan ilmin ya kuma yi bayani sport da shirin da gwamnati ta ke yi na bude makarantu, ya ce za a rika yin darusa da rana da nufin rage cunkoso.

What's On Your Mind?