Batun Takarar Manyan Kasashen Duniya A Nahiyar Afirka Da Amurka Ta Tabo Zai Haifar Da Illa Ga Moriyar Kasashen Afirka

0
103

Batun Takarar Manyan Kasashen Duniya A Nahiyar Afirka Da Amurka Ta Tabo Zai Haifar Da Illa Ga Moriyar Kasashen Afirka

Daga CRI Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi nuni a yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, idan kasar Amurka tana son yin takara tsakanin ta da manyan kasashen duniya a nahiyar Afirka, tana kuma son kawar da saura, hakan zai haifar da illa ga kasashen nahiyar ta Afirka.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a jiya sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, ya zanta da shugaban kasar Kenya da ministan harkokin wajen kasar, da kuma shugaban tarayyar Najeriya da ministan harkokin wajen kasar ta kafar bidiyo, kana ya yi ziyara ta kafar bidiyo a wasu asibitoci da kamfanonin samar da makamashin da ake sabunta amfani da su, wadanda kasar Amurka ta taimaka wajen gina su.
Recreation da hakan, mukaddashin mai bada taimako ga sakataren harkokin wajen kasar Amurkan, mai kula da harkokin Afirka Robert Godec, ya bayyana wa kafofin watsa labaru cewa, Amurka ta shaida wa jama’ar kasashen Afirka cewa, idan aka kwatanta tsarin bunkasar tattalin arziki da Sin ta aiwatar a nahiyar Afirka, tsarin Amurka ta fi maida hankali ga moriyar nahiyar Afirka, da kara jawo hankalin kasashen Afirka.
Recreation da wannan tsokaci, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, a sakamakon tinkarar cutar COVID-19, kasashen Afirka da dama suna fuskantar sabon kalubale. Kuma Sin tana fatan kasa da kasa ciki har da kasar Amurka, za su dora muhimmanci ga batutuwan da Afirka ke kula da su, da daukar matakai, da kara nuna goyon baya wajen taimakawa kasashen Afirka, a fannin tinkarar kalubale da samun bunkasuwa.
Ya ce idan kasar Amurka tana son yin takara a tsakaninta da manyan kasashen duniya a nahiyar Afirka, tana kuma son dakatar da saura, hakan zai kawo illa ga kasashen Afirka, kuma kasashen Afirka da jama’arsu ba za su amince da ita ba.
Zhao Lijian ya bayyana cewa, Sin tana girmama burin jama’ar Afirka, da yin kokarin biya bukatun kasashen nahiyar. Har ila yau dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ya taka muhimmiyar rawa wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da kasashen duniya.
A cikin shekaru fiye da 20 da kafa wannan dandali na tattaunawa, yawan kudin ciniki tsakanin Sin da Afirka ya karu da ninki 20, kana yawan jarin da Sin ta zubawa Afirka kai tsaye, ya karu da ninki 100, wanda hakan ya amfani jama’ar Sin da na kasashen Afirka. (Zainab)

What's On Your Mind?