Batagari Sun Banka Wa Ofisoshin INEC 3 Wuta A Ebonyi

- Advertisement -

Batagari Sun Banka Wa Ofisoshin INEC 3 Wuta A Ebonyi

Wadansu mutane wadanda ba a san ko su waye ba solar banka wa ofisoshi uku na Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) wuta a Jihar Ebonyi a yau Laraba.

Ofisoshin su ne na ƙananan hukumomin Ezza ta Arewa da Izzi.

Jami’in Yaɗa Labarai na INEC a jihar, Mista Cornelius Ali, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a Abakaliki, ya ce ɓatagarin da su ka aikata hakan solar ƙone ofisoshin tare da injinan janareto da rumfunan zaɓe da wasu muhimman kayayyakin zaɓe.

Ya ce shugabannin hukumar solar kai ziyarar gani da ido zuwa ofisoshin da gobarar ta shafa da nufin sanin yawan ɓarnar da aka yi.

Sai dai ya kwantar da hankali kan fargabar da ake yi kan ko wannan ɓarna za ta kawo barazana ga shirin da ake yi na gudanar da aikin rajistar masu zaɓe wanda za a yi a watan Yuni.

Mista Ali ya ce, “A safiyar yau, mun samu rahoton cewa wasu mutane solar kai hari tare da banka wa ofisoshin mu na ƙananan hukumomin Ezza ta Arewa da kuma Izzi wuta, inda su ka lalata muhimman kadarorin hukumar.

“Da mu ka je can, mun ga an ƙone gine-ginen da ofisoshin mu ɗin ke ciki yayin da kuma an ragargaza injinan janareto da rumfunan zaɓe da sauran kayayyakin INEC da ke cikin waɗannan ofisoshin baki ɗaya.”

Kakakin hukumar ya ƙara da cewa ɓatagarin solar ja wa hukumar babbar asara, to amma ya ce harin ba zai rage mata ƙwarin gwiwa ba wajen sauke nauyin da aka ɗora mata na yi wa jama’a aiki.

Ita kuwa da aka tuntuɓe ta, Jami’ar Yaɗa Labarai ta Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ebonyi, Missis Loveth Odah, cewa ta yi aiki ya yi mata yawa, ba za ta iya magana da ‘yan jarida ba.

- Advertisement -