Barista Ahmad Ghazali Ya Zama Abin Koyi -Mansur Dandago

0
63

Barista Ahmad Ghazali Ya Zama Abin Koyi -Mansur Dandago

Watan Azumi na cikin lokutan da mawadata da ‘yan kasuwa kan bayar da gagarumar gudunmawa wajen saukakawa al’umma ta kowacce fuska, musamman bangaren kayan bukatar yau da kullum da suka shafi tufafi da abinci.

Wannan tasa jama’a kullum ke sawa matashin dan Kasuwa mai kishin ganin talaka ya samu rangwame, ya rungumi  shirin saukakawa kan duk abubuwan da yake sayarwa domin ganin shi ma ya bayar da tasa gudunmawa kamar yadda ma’aiki ya yi umarni albarka. Ambasada Mansur Haruna Dandago Jamai’in yada Labaran kungiyar Kasuwar Kantin Kwari dake Jihar Kano ne ya yi wannan tsinkaye lokacin da yake zantawa da MOBILIZED9JA A Yau.

Mansur Haruna Dandago ya ce akwai matasan ‘yan Kasuwa dake tasowa da kuma wadanda tuni suka shahara ta fuskar kasuwanci a wannan kasuwa ta Kwari, wanda wannan matashi Barsita Ahmad Ghadali shugaban rukunin kamfanonin Muwaffak Have an effect on  ke shugabanta ya yi fice musamman ta fuskar daukar matasa aiki, wanda zuwa yanzu akwai sama da mutun 100 dake gudanar da ayyuka iri daban-daban da rumfunan wannan kamfani dake ciki da zagayen kasuwar ta Kantin kwari, wadanan mutane kowa na aiki  kuma yana samun abin sawa abakin salati.

Ya ce wani abin sha’awa da ba ko da yaushe ake katarin cin karo da irinsa ba, shi ne yadda duk wanda ke aiki a karkashin wannan bawan Allah Barista Ahmad Gharzali kullum yana da kwanon abincinsa idan ya fito kasuwa, babu batun sayen abinci, sannan kuma ga kulawar da ma’aikata ke samu, wanda hakan tasa jama’a ke sa albarka cikin al’amuransa.

Haka kuma a wannan kamfani an horar da ma’aikata kyakkyawar mu’amala da abokan cikinsu, wanda wannan ta sa jama’a ke ta tururuwa domin hada alaka da wannan kamfani musamman ganin yadda ake mutunta dan adam.

Bidiyo: Ansaki video sadiya haruna tare da wata wanda mutane suke zargin iskanci suke yi

Da aka tambayeshi ko me wannan matashin dan kasuwa ya shahara ta fuskar kasuwanci. Mansur Haruna Dandago ya ce wannan matashi ya shahara wajen sayar da tufafi da suka hada da Leshi, Atamfa, Riguna da sauran kayan amfanin mata da maza da kuma yara, yana da kantina birjik a ciki da zagayen kasuwar ta Kwari.

Sannan kuma ganin an shiga wannan wata mai albarka, shugaban wannan Kamfani ya samar da rangwame akan dukkan abubuwan da yake sayarwa domin saukawawa abokan cinikayyarsu.

Daga nan sai Mansur Haruna Dandago ya bukaci sauran ‘yan kasuwa da su yi koyi da wannan kyakkyawar tarbiyyar wannan matashi, musamm  an yadda yake samar da gurabun aikin yi, da kuma uwa uba biyan dukkan harajin Gwamnati, wannan kuma shike nuna kishin jiha da kasa baki daya.

Lallai akwai bukatar sauran ‘yan kasuwa kowa ya taho domin kamanta rikon amana da gaskiya, ya ce duk halin da ake ciki babbar matsalar dake haifar mana da matsaloli bai wuce rashin rikon amana da kamanta gaskiya ba. Don haka mu a kungiyance muna tabbatar wa da jama’a cewar ako da yaushe muna fatan samun ire-iren wadannan matasa masu kaunar cigaban Jihar Kano da kasa baki daya.

What's On Your Mind?