Barazanar Tsaro A Nigeria Bayan Faduwar Katangar Chadi, Idris Deby

0
212

Barazanar Tsaro A Nigeria Bayan Faduwar Katangar Chadi, Idris Deby

Na tuna lokuta da dama da Shugaban yake fitowa da kansa wajen ganin ya yaki yan tawayen cikin kasar sa wacce tayi shuhura wajen yawaitar yan tawaye da suke fada da Gwamnatin kasar. Rikicin kasar Chadi ya bada dama wajen yaduwar makamai a yankunan Afrika musamman kasashen da suke cikin irin lalurar ta rashin tsaro da yan tawayen cikin gida, irinsu Mali, Sudan, Nigeria da Libya. Kuma Marigayi Deby ya kasance daya daga cikin Shugabannin yankin Afrika daya jajirce wajen ganin an kori yan ta’adda a yankin na Afrika.

Tabbas mutuwar sa babbar barazana ce a irin wannan lokacin da ake ciki.
Kwana daya kenan da aka bayyana cewa Shugaba Deby ya Kuma lashe Shugabancin kasar ta Chadi. Kwana daya tsakani kuma ya rigamu gidan gaskiya bayan raunin dayaji alokacin fadansa da yan tawayen FACT.

Kwamanda Deby ya Jagoranci mulkin kasar tun shekarar 1991. Ya kasance tsayayyen namiji wanda ya dinga fada da yan tawaye da masu fafutukar kafa Dimokradiya a kasar irinsu MDD (Mobement for Democracy and Debelopment). Yana daya daga cikin Shugabannin Afrika wanda yafi fuskantar barazanar juyin mulki, a shekarar 2006 ma har karamin jirginsa aka rawaito cewar an harbo, amma kuma bai mutu ba.

Yana daya daga cikin Shugabannin da suka dinga fada da Omar Bashir na kasar Sudan, tare da zargin kasar da goyon bayan yan tawayen Chadi. Wanda har sai information kai solar yanke duk wata alakar diflomasiyya tsakanin su. A watan Agustan 2006 ne ranar rantsar dashi cin mulki zango na uku, Shugaban kasar Sudan ya hallaci rantsuwar, wannan itace ta kawo karshen rikicin su, ta kuma dinke barakar dake tsakanin su har suka dawo da duk wata alaka tsakanin kasa-da-kasa.

Akwai zarge-zarge masu yawa akan Shugaba Deby musamman wanda suka danganci cin hanci da rashawa. A shekarar 2006 Jaridar Forbes ta sanya kasar Chadi a matsayin Kasa ta farko a duniya da cin hanci yayi kakagida. Daga sannan ne Shugaba Idrisa ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa, mai taken ‘Operation Cobra’, wanda aka rawaito cewar hakan ya sanya Shugaban ya kwato akalla dalar amurka miliyan hamsin daga hannun yan Jari hujjan kasar. A shekarar 2016 kasar ta kasance ta 147 cikin kasashe 168 da sukai shuhura wajen cin hanci da rashawa kamar yadda Transparency Worldwide ta futar.

Shugaba Deby ya farfado da arzikin kasar, bayan gano danyen man fetur da akayi a kasar wajejen shekarar 2000. Bankin Duniya tare da hadin gwuiwar Chad-Cameron Petroleum Debelopment ne suka dinga aikin hako man, wanda kasar take amfana da kaso 12.5 kawai, wanda hakan ya bawa Kamfanunnuka da dama na kasashen ketare sanya hannun jarinsu a kasar. Marigayi Deby yayiwa Bankin Duniya tawaye da cewar kason da ake bawa kasar yayi kadan, wanda hakan yasa ya koma kaso 60 cif cikin 100. To amma Bankin na Duniya kuma sai ya ayyana janye wannan kason, tare da zargin cewa Deby yana amfanin da kudaden ne kawai wajen kafa karfin Gwamnatin sa, ba hidimtawa kasar ba,wanda daga karshe aka sasanta, kuma kasar ta dinga amfana da kudaden arzikin kasar kai tsaye.

Gwamnatin Deby cike take da kalubale musamman wanda ya danganci yan tawaye, juyin mulki da kuma kungiyoyi masu fafutukar neman yanci da Dimokradiya. Hakan ya sanya kasar take da yawan Jami’an tsaro, wanda da yawan lokuta Deby da shi ake futa wajen gabzawa da yan tawaye a matsayinsa na Soja. Sojojin kasar sa solar temaka a yankin Darfur, Afrika ta tsakiya (Central Afrika), Mali da kuma Yakar yan Boko haram. Wannan ta sanya kasar take cikin hadakar Sojojin kasashen Nijar, Nijeriya, Benin da kuma Kamaru, wanda ake kira Multinational Joint Job Drive (MNJFF), wanda suke da fada da yan tawaye da sauran yan ta’adda.

Yan tawayen da ake kira FACT da harshen Faransanci (Entrance For Change and Harmony In Chad) sune sukayi masa raunin daya janyo ajalinsa, wanda majiya tace yaje kaiwa Sojojin kasar dake yaki da yan tawayen ne ziyara, rikicin ya afku wanda ya kawo karshen mulkin sa, wanda wasu suke ganin yayi kaka-gida da tsaurarawa duk wadanda ba Gwamnatinsa suke yiwa biyayya ba.

Lokacin da akayi taron Kungiyoyin Kasashen Afrika a Addis Ababa wanda Shugaban kasar Afrika ta Kudu yake jagoranta. A wannan taro kasashen solar tattauna hanyoyin kawo karshen ta’addanci a nahiyar Afrika, mai taken ‘Silencing The Gun In Africa’, to amma babban abin damuwar shine wanda har kawo yanzu babu abinda ya canza sai ma karuwa da yayi. Kusan kullum karfin yan ta’addan yana karuwa ne yadda suka gagari Gwamnati, kuma suke janyo asarar dinbin al’ummar da basu ji, kuma basu gani ba.

Nijeriya na daya daga cikin wanda sukafi kowa shiga irin wannan kalubalen, wanda kusan banda taimakon MNJFF din, da tuni Boko haram solar kuma gagarar Gwamnatin kasar nan. A yanzu idan ka dauke Boko haram, ta’addancin garkuwa da mutane a Arewacin kasar da kashe-kashe na babu gaira babu dalili sune mafi muni a cikin kasar yanzu. Ko a wannan satin da muke ciki an sace dalibai a Jihar Kaduna, an kashe wasu mutane a Jihar Zamfara sama da mutane dari. Wannan fa shine abinda kullum ke faruwa a cikin kasar.

Dole ne sai kasashen Afrika solar hade kansu a wannan lokacin musamman bayan mutuwar Idris Deby, solar tabbatar da cewa shirin su na ‘Silencing The Gun’, ya cimma nasarar da suke bukata. Rashin cimma nasarar wannan shiri babbar barazana ce ga kasashen dake cikin wannan ibtila’in, domin yan ta’addan yanzu solar samu karfin gwuiwar da suke ganin zasu iya fafatawa da kowace iriyar Gwamnati, kuma suci nasara. Sannan kin daukar matakan gaggawa zasu sanya kara yaduwar makamai tsakanin yan ta’addan. Da yawan lokuta mutane na tambayar shin ta wace hanya yan ta’addan ke samun makamai masu hatsari. A duk lokacin da Shugaban Kungiyar Boko haram ya saki wani faifan bidiyo, zaka gansu dauke da mugayen makaman da su kansu jami’an kasar nan zakaga basu mallakesu ba. Wanda hakan yana kara sanya tsoro ga al’ummar kasar nan.

Na sha fada cewa Gwamnati tana sako-sako da fada da yan ta’addan Boko haram da sauran masu garkuwa da mutane, wannan ta sanya da yawan lokuta nike goyon bayan a fatattaki duk masu garkuwa da mutane, da ace Gwamnati tayi sulhu dasu. A baya Gwamnatin Jihohin Katsina da Zamfara sunyi hakan, amma kuma bai amfanar da komai ba. Gwamnati dole ne tayi duk me yiwuwa ganin kawai taga karshen duk wani dan ta’adda a cikin kasar nan, tare da hukunta duk wanda suke hannunta, ko kuma gafartawa wanda suka ajjiye makamansu bisa radin kansu, tare da amfani dasu wajen gano sauran yan ta’addan da suke barazana ga tsaron kasar mu.

Allah ya kawo mana zaman lafiya a nahiyar Afrika, da kuma kasarmu Nijeriya.

What's On Your Mind?