Barazanar Cutar Koda A tsakanin Al’ummar Arewa Maso-gabas

0
98

Barazanar Cutar Koda A tsakanin Al’ummar Arewa Maso-gabas

Matsalar yawaitar masu kamuwa da cutar koda kuma take nema ta gagari kundila, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubun-dubatar al’umma fiye da kowace cuta.

Wannan filin ya samu zanta wa kwararrun likitoci, wadanda ke fama da wannan lalura ta cutar koda a jihohin Borno da Yobe. Bugu da kari kuma da matakan da ake dauka domin dakile yaduwar ta tare da shawarwarin likitocin.

A cikin lokuta da dama, jama’ar wannan yankin suna fargaba tare da shaukin sanin hakikanin abubuwan da ke jawo yawaitar kamuwa da cutar koda a jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Taraba da Bauchi.

Wanda Farfesa Ibrahim Ummate, shi ne shugaban cibiyar kula da masu fama da cutar koda a asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri, a wata tattaunawar da nayi dashi ta wayar tafi-da-gidan ka, ya bayyana wasu muhimman abubuwan da binciken su ya gano, wadanda suke da alaka da kamuwa (haifar) da cutar koda, da suka hada da matsalar hawan-jini, cutar sikari da sikila, kwayoyin hallita na gado, tare da shan maganin asibiti da na gargajiya ba bisa ka’ida ba, da makamantan su.

Dr. Ibrahim Ummate ya sake bayyana cewa, akalla kowane mako cibiyar kula da masu cutar koda a asibitin, ta na karbar sabbin wadanda suka kamu da wannan cutar ta koda 50 daga jihar Borno, sannan da kwatanjwacin hakan daga jihar Yobe.

Ya sake fayyace cewa, a shekarun baya, wannan cibiya tasu ta babbar asibitin koyarwar jami’ar Maiduguri ta gudanar wa kimanin majinyata 1,854 wankin koda; tsakanin 1999 zuwa 2018, wanda hakan ke nuna cewa a kowace shekara suna yiwa mutane 98 wankin kodar.

“wanda wannan cibiyar ta na kula da majinyatan da suka fama da cutar kodar da suka fito daga baki dayan yankin arewa maso-gabas, da wani yanki na kasashen makwabta; na Kamaru, Chadi da Nijar”. Inji Dr Ummate.

“wanda bayan da aka kirkiro jihohin Yobe, Adamawa, Gombe, Bauchi tare da Taraba, inda suma suna da nasu cibiyoyin kula da majinyatan, kuma duk da suke da wadannan cibiyoyin, amma dai har yanzu ta na kula da kaso 50 dikin dari na masu dauke da jinyar, kuma har yanzu wadannan jihohin yankin arewa maso gabas tare da kasashen makwabta suna amfani da wannan dama wajen kawo majinyata.

Ya ce a shekarun baya, jihar Borno ta na adadin masu fama da cutar kaso 39 sai Yobe 32, Adamawa 17, Bauchi da Gombe, kowanen su kaso 5; inda Taraba mai kaso 2, wanda wannan ya nuna har yanzu kaso 50 cikin dari na masu fama da matsalar solar fito ne daga arewa maso gabas ne.

Dr Ummate ya kara da cewa, kaso 68 cikin dari na majinyatan da wannan cibiya ke kula dasu maza ne, yayin da kaso 32 ne mata.
Dangane da yanayin shekarun masu kamuwa da cutar kodar, ya ce cutar ta na kama masu shekaru; kama daga 40 zuwa 49 (kaso 39), 30 zuwa 39 (kaso 24), 20 zuwa 29 (kaso 27), 50 zuwa 59 (kaso 14), 60 zuwa 69 (kaso eight), sai kasa ga shekara 19 (kaso 6), wanda yan sama da shekaru 70 (kaso 2) kacal.

Har wala yau kuma, ya bayyana cewa, cibiyar kula da masu cutar, ta babbar asibitin koyarwar, ta na da na’urorin wanke kodar har 15, kuma ya ce ita ce ta fi kowace cibiya a yankin.

Haka kuma, ya ayyana cewa, har yanzu yankin arewa maso gabas yana matakin tsaka-tsaki ne, idan an yi lura da adadin masu dauke da cutar a fadin Nijeriya.
Farfesa Ummate ya kara da bayyana cewa, a matsayin su na kwararru a fagen, suna iya kokarin lalabo matakan dakike yazuwkr cutar tare da fadakar da jama’a ta hanyoyin kafafen yada labarai, domin daukar matakan kariya daga wannan hattsabibiyar cutar.

Radi: Budurwa Ƴar Arewa Ta Roƙi Mahaifin Ta Yayi Mata Aure, Ko Na Dole Ne

Ya bayar da shawara kan cewa su rinka zuwa asibitocin da ke kusa dasu, domin gudanar musu da gwaje-gwajen cutukan sikari, hawan jini, kuma su guji shan magunguna ba bisa ka’ida ba.

A hannu guda kuma, kwamishinan kiwon lafiya a jihar Yobe, Muhammad Bello Kawuwa ya bayyana wasu matakan da gwamnatin jihar ke dauka wajen dakile kaifin matsalar.

Ya ce abu na farko shi ne, bayan matakan fadakar da jama’a dangane da yanayin wannan matsalar, gwamnatin jihar Yobe ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar lamarin da muhimmanci na cutar koda, kuma ta yi alkawarin yiwa masu fama da ita wankin kodar kyauta, a duk fadin jihar Yobe.

“Abu na biyu kuma shi ne, idan so samu ne a yi dashen kodar, wanda gwamnati ta na kokarin samar yanayin da za a rika yiwa jama’ar wannan jihar dashen kodar. Wanda yanzu haka maganar da muke da kai gwamnatin jihar Yobe ta cimma yarjejeniya da wata asibitin koyarwa a jami’a a Kairo- Misra, wadanda suka kware a dashen koda, ta hanyar musayar yadda zamu fara aikin dashen kodar”.

“Wanda duk wannan ba shi bane, babban abinda ya dame mu shi ne samun tabbacin me ye ke kawo wannan matsala ta gazawar koda, domin fadakar da jama’a su guje shi”.
“Wanda a matakin farko na binciken da ke hannun mu shi ne, yadda mutane ke amfani da wasu magunguna a lokacin ajiya ko busar wa, da wasu kayan da ake hada burodi dasu- duk suna da alaka da wannan matsalar.

Kuma mun riga mun dauki matakan fadakarwa tare da hadin gwiwa da hukumomin kula da abinci na kasa da masarautar Bade da sauran su”.

Dr Kawuwa ya ce, “kuma akwai wani binciken kwakwafa na kimiyya wanda mun riga mun fara shi, don gano hakikanin matsalar. Kuma in sha Allahu zamu tabbatar wajen ganin idan akwai karin wasu bayanai kan na farko, don mu bayyana wa gwamnati domin daukar mataki, su kuma jama’a su yi kokarin kauce musu”.

Dangane da kara wa jama’a kwarin gwiwa, ya ce “kuma kwarin gwiwar da zan kara bayyana wa jama’a shi ne gwamnatin mai girma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ta tausaya jama’a dangane da yadda suke jimamin wahalar wankin koda, wanda kusan komai karfin ka sai ka jijiga ka, saboda yadda dole kowane sati sai ka kashe naira 50,000- ka ga ba karamin aiki bane”. Inji shi.

What's On Your Mind?