Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

0
98
  • Karfin hali ya kai wani matashi mai suna Kabiru shiga majalisar dokoki sata

  • Bai sani ba ashe na’urar CCTV na daukansa yayinda yake devil

  • Tuni an damke shi kuma an sanar da jami’an tsaron majalisar dokokin dake Abuja

Wani matashi mai suna Kabiru a ranar Juma’a ya fasa cikin majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki.

Wannan abu ya faru misalin karfe 2:30 na rana inda matashin yayi amfani wani mukulli na daban.

An yi zargin Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu na’urar kwamfuta, na’urar fotocofi da printer.

SaharaReporters ta tattaro cewa Kabiru ya kasance hadimi ga wani dan majalisa daga Adamawa kuma sannanen mutum ne a majalisar.

Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki

Jami’an tsaron majalisar solar gane fuskarsa a bidiyon na’urar CCTV da ta daukeshi yana fashin.

A yayinda ake tattara wannan rahoton, wasu yan majalisa wanda ya hada da mai magana da yawun mambobin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, na wajen da aka kama matashin.

Yadda Zazzau Da Zazzagawa Suka Karbi Sabon Sarkinsu

An samu labarin cewa dan majalisar da matashin ke yiwa aiki yana kokarin ganin an yi rufa-rufa kawai a manta da lamarin.

Bidiyon na’urar CCTV ya nuna matashin lokacin da yake devil.

A wani labarin mai tashe, Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa, ya daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin wata babbar kotun tarayya wacce ta ci tararsa naira miliyan 50 a kan cin zarafin wata mata.

A 2019, ‘yan sanda solar gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, a kan zarginsa da laifin cin zarafin wata mata mai suna Osimibibra Warmate a wani shago a Abuja.

What's On Your Mind?