Bankin CBN Zai Habaka Noman Masara Don Habaka Kiwon Kaji

0
135

Bankin CBN Zai Habaka Noman Masara Don Habaka Kiwon Kaji

A kimanin watanni sha biyar da suka gabata, fannin kiwon Kaji  a  Nijeriya ya  fuskanci dimbin matsaloli,  musamman ganin yadda masu yin sana’ar suka tabka dimbin asara bayan barkewar annobar Korona da ta janyo tashin farashin abincin kajin.

Masu yin sana’ar dai sune abin ya fi yiwa illa,  nusamman ganin yadda hakan ya janyo wasu manyan masana’antun dake yin sana’ar suka dakatar da ita wasu kuma suka dinga yanka Kajin  da suka kamu da matsalar karancin abinci mai gina jiki,  domin su fuskanci matsalar tsadar kiwon Kajin da tsadar abinci abincin su wanda shi ne babbar madogara a fannin na kiwo Kaji .

Biugu da kari,  kasancewar Nijeriya a matsayin uwa a nahiyar Afrika  wacce ta kasance mai dimbin alumma,  yawan masarar da ake samar wa a yakin ya ragu a shekarun da suka gabata,  musamman saboda matsalar dumamar yanayi da  yawan kai hare-hare da kuma annobar Korona.

A bisa wata kididdigar da aka samo daga ma’aikatar aikin noma da raya karkara,  yanzu haka,  Nijeriya na fuskbtar karancin  Masara da ta kai kimanin tan miliyan  10.5 a duk shekara sabanin bukatar da ake da ita ta tan miliyan 15, unra kuma ake da gibin da ya kai na tan miliyan  four.5a duk shekara.

Har ila yau kuma,  sashen  bunkasa aikin noma  na kasar Amurka (USDA) a a cikin rahotaonsa na amfanin gona na shekarar  2020 ya dora tsakiyar shekara ta 2020 zuwa 2021 ta Nijeriya  kan noman Masara  cewa,  ya kai tan miliyan   9, inda  ta ragu da  kashi  13, idan aka kwatanta da tan miliyan   11.5 da aka yi kirdado a shekarar da ta wuce.

Za Mu Cigaba Da Gudanar Da Taron Bajekolin Noman Albasa

Karancin da aka samu na samar da Masarar a shekarar   2019 da shekarar  2020 ya tilsta  farashin  na Masarar  karawa zwa naira  250,000 na ko wanne tan daya,  inda hakan ya haifar da babbar barazana ga masanaantun na kiwon Kahin gidan gona da ka ga sauran masana’antun dake sarrafa Masara zuwa wasu kayan abinci harda karancin ta a kasar nan.

Shugaban kungiyar masu kiwon Kajin gidan gona    (PAN) reshen jihar  Delta  Alfred Mrakpor ya sanar da cewa,  hauhawan farashin na Masarar yana kara zamowa barazana ga  masu kiwon Kajin gidan da dama da kuma ga masana’antun dake sarrafa abincin kajin,  inda kuma hakan ke kara sahafar tattalin arzikin kasar nan.Mrakpor ya kara da cewa,  hauhawan farashin na Masarar ya nefa tsoro ga zukatan masu yin sana’ar  da kumaa tsakanin masu sarrafa abincin kajin a kasar nan.

A cewarsa,  hakan ya kuma janyo ‘yan Nijeriya da dama,  ba sa iya sayen kwan Kajin gidan gona a yanzu da kuma Kajin achieve cewa,  daukacin farashinsu,  ya tashi da kusan kashi   50.

A bisa kokarin samar da sauki ga ‘yan Nijeriya  na karancin Masarar a kasar nan,  tuni  CBN  ya fara rabar da tan-tan na Masara 300,000 ta hanyar shirin aikin noma na  Anchor Debtors da kuma ta hanyar sauran dabarun aikin noma.

Kan fitarwar da tan 50,000 na Masarar ta farko da CBN ya yi a kwanan baya,  hakan ya taimaka wajen saukar farashin na Masarar a kasar nan.

A bisa wani bincike da jaridar  BusinessDay ta gudanar a wasu manyan kasuwanni dla jihar  Lagos,  hakan ya nuna cewa an sayar da  tan na Masara kan naira 250,000 a watan Janairu,  inda a yanzu,  ake sayar da kowane tan daya kan naira  180,000.

Babban Shugaba na sashen mulki da hudda da jama’a na kamfanin  Amobyng Nigeria  Dakta  Agboola Belgore, ya jinjina wa   CBN kan fitar da tan  50,000 na Masarar ga manyan masana’antun dake sarrafa Masara a Nijeriya,  inda kuma ya yi kira ga CBN kan ya ci gaba da bayar da irin wannan daukin.

Ya ci gaba da cewa,   a ra’ayina farashin kar haura naira  130,000 na ko wanne tan daya,  inda a na yanzu,  ya kai naira  180,000 na ko wanne tan  daya.

A cewarsa,  bisa ga wannan labarin na samar da daukin na  “ CBN, farashin na Masarar ya daina tashi,  musamman saboda fitar da tan 50,000 na Masarar,  inda hakan ya karya farashinta zuwa kimanin naira  180,000 na ko wanne tan daya   kuma masana’antun dake sarrafa Masara da kuma masu kiwon Kaji gidan gona duk solar yi maraba da hakan”.

Ya bayyana cewa,  ya yi imanin cewa,  idan aka kara fitar da wani tan 300,000 na masarar a a zagaye na biyu,  hakan zai taimaka matuka wajen karya farashinta.

What's On Your Mind?