Ban San Makomata Ba A Real Madrid – Bale

0
69

Ban San Makomata Ba A Real Madrid – Bale

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale, wanda yake zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, ya bayyana cewa har yanzu bai san makomarsa ba a kungiyarsa ta kasar Spaniya.

A ranar Lahadi ne Tottenham ta yi nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Sheffield United da ci Four-Zero a wasan mako na 34 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi kuma hakan  ya kara kwarin gwiwa ga kungiyar kan fatan da take yi na son buga gasar Zakarun Turai ta badi.

Tun kafin hutun rabin lokaci dan wasa Gareth Bale ya fara cin kwallo, bayan da suka yi hutu suka koma karawa ta biyu ne ya kara biyu a ragar Sheffield United sannan Tottenham ta kara na hudu ta hannun Heung-min Son, saura minti 13 su tashi daga fafatawar.

dan kasar Koriya ta Kudu ya ci wata kwallo minti biyar da komawa zagaye na biyu, amma alkalin wasa ya kashe ta cewar ya yi satar gida kuma da wannan sakamakon Tottenham tana mataki na biyar da tazarar maki biyar tsakaninta da ta hudu Chelsea, kuma saura wasa hurhudu a karkare kakar bana.

Ita kuwa Sheffield United wadda ta fadi daga buga gasar Premier ta badi tun 17 ga watan Afirilu, bayan da kungiyar kwallon kafa ta Wolbes ta doke ta, ta kai hari daya tal a ragar Tottenham.

Kuma mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Hugo Lloris bai fuskanci wani kalubale ba kaco kan din fafatawar kuma wannan ne karo na biyu da Bale ya ci kwallo uku rigis a tarihin Premier League, bayan da ya fara a kan Aston Villa tun cikin watan Disambar 2012.

What's On Your Mind?