Bambancin Sarakunan Baya Da Na Yanzun – Daga ’Yar Shekara 123

0
23

Wannan zantawa ce da LEADERSHIP A YAU ta yi da wata dattijiya, Banufiya, mazauniyar garin Kaduna na tsawon zamani, HAJIYA FATIMA BANUFIYA, mai shekaru 123 da watanni da haihuwa a cikin wannan Duniyar.

Bambancin Sarakunan Baya Da Na Yanzun Daga ’Yar Shekara 123

Hajiya Fatima ta yi magana ne a kan yanayin garin Kaduna a wani zamani na can dauri, da kuma bambance-bambancen da zamani ya kawo walau ta fuskar al’umma ko kuma ta fuskar shugabannin al’ummar. Wakilin LEADERSHIP A YAU, UMAR A HUNKUYI, ne ya zanta da ita a gidanta da ke Anguwar Rigasa a Kaduna. A sha karatu lafiya:

Zuwa na garin Kaduna: Na jima a garin nan, tun kafin a bai wa Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris sarauta, domin yanzun ina da shekaru 57 kenan da zama a garin nan, watau zuwana na baya kenan, amma zuwana na farko garin nan daga layin Shaba sai anguwan Lebura. Ka ga inda asibitin janaral din nan yake, gidan Gwari ne, muna zuwa suna noma rake, suna noma doya, suna noma rogo. Shi kuwa Shaban nan da ake cewa layin Shaba, mijin yayata ne, har ma photo voltaic haihu da shi. Shi ne kuma babba a cikin ma’aikatan da suke aikin titin dogo na Jirgin kasa. A lokacin da aikin ya kawo su garin nan ne sai ya ce shi yana sha’awan garin nan, dalili kenan da aka kafa ma shi bukka a nan layin Shaba.

Shi kuma anguwar Leburori din nan ita ce Tudun Wada a halin yanzun, leburori ne da karuwansu da masu kuntiginsu da dai duk karikitansu duk tattare a wajen. Wannan shi ne asalin Layin Shaba, kuma da asalin Anguwar Leburori, watau Tudun Wada kenan a halin yanzun. Wanda a lokacin da na zo garin nan ina budurwa ni dai in baccin wadannan layukan guda biyu to ni ban san wani layin ba kuma. Amma kasuwan Central tana nan, nan ne dai kasuwar, a lokacin akwai bukkoki na kara guda uku a cikinta, in kuma baccin su babu wani abu a cikinta. A lokacin na ma tambaya kan wadannan bukkokin, aka ce mani na wasu mahauta ne masu kudi suka yi saboda ruwan sama, in ruwa ya zo a ciki suke shiga suna fakewa. Saboda haka muna kara yi wa Allah godiya.

CBN – Mu Na Samar Da Tsarin Yakar Koma-Bayan Tattalin Arziki

Duniya budurwar wawa ce: Ita dai Duniya budurwa ce kamar yanda kuke cewa, Duniya budurwar wawa, yau ta dauki wannan ne gobe ta yar da shi, gobe kuma wani za ta dauka jibi kuma ta kuma jefar da shi. A lokacin da aka yi yakin Hitla na Jamus, ina da shekaru 15 a Duniyar nan, don haka a halin yanzun ina da shekarun haihuwa a Duniyar nan 123 da watanni hudu cur, in ka sami sarari ka yi cakin ka gani da kanka, don haka ni na godewa Allah.

Kafa Anguwar Rigasa: A zamanin baya can muna nan zaune a Unguwar Tudun Nupawa aka zo ana ta bamu hakuri da cewan za a rabar da fili a wani daji wanda aka sanya masa suna Rigasa, a kan fam bibbiyu, watau Murtala hudu ga duk mai shi kuma mai bukata, ga shi nan ka je ka diba iya bukatarka, amma ka ga iyakacin inda Allah ya hore mani a nan, ga shi yanzun ni da kai muna zaune a cikinsa. Domin a lokacin na sayi wuri photo voltaic kai biyar, amma sai ‘yan’uwana Nupawa suka rika zunde na wai na sayi wuri a kungurmin daji zan je barayi su kashe ni, sai na bi duk na sayar da su, da Allah ya kaddara haka za a yi.

Bambancin Sarakunan da, da na yanzun: Bambancin Sarakunanmu na da, da na yanzun yana da yawa, na yanzun ko an ba su shawara ba dauka suke yi ba. Sarki Umaru Sanda Ndayako, Allah ya jikansa, idan dare ya yi yakan yafa mayafi ya shiga cikin gari da kansa shi kadai yana zagawa, saboda fadawa sukan zo suna ce masa ranka shi dade ban da yabonka ba abin da ake yi, wanda shi kuma ba ya yarda da hakan. To in ya yi irin wannan fitan ya je wani wajen sai ya ji ana hira ana cewa, ai mu Sarkin garin nan namu mun shiga uku, yanzun an ce har saniya ta shinkafa ta zama Nai? Kuma Sarki yana ji yana gani? Wannan wane irin Sarki ne! sai ya ji wannan da kunninsa. To sai da protected in ya fito majalisa fadawa photo voltaic zo suna ce masa, ranka shi dade ai in ban da yabonka babu abin da ake yi, sai ya ce munafukan Allah, azzalumai shari’a ta da ku sai a gobe kiyama.

Gidajen Sarautar Nupawa: Akwai Kakana da ake ce ma Muhammadu Awwalu, mu kuma asalinmu da ake cewa Nupawa banza Bakwai, sune banza Takwas, Nufawa Sakkwatawa ne da Kabawa, da Gwandu. Wadanda suke Nupawan asali, su ne su Usman Babafategi, watau su Samanja mazan fama, su ne asalin Nupawa, amma Bida garin Basangai ne, su garin su Samanja Fatigi suka zo suka cinye su da yaki, a sannan ba sa Sallah. Babban Masallaci na farko na Bida na yanzun, na kofar Sarki Bello, nan ne babban dakin tsafi.

Sai Sakkwatawa suka ce, su wadannan mutanan da suka ci garin ga, su ma ba Sallar suke yi ba, mu je mu far masu ba sai mun aike masu da takarda ba. mu kira makwabtanmu biyu, Birnin Kebbi da Gwandu, suka kira su suka kuma zo suka shiga suka far masu.

Hakan shi ya sanya a halin yanzun in ka je Bida gidan Sarakuna uku ne. akwai gidan Sarki Abubakar wanda ya yi fada da Bature, nan ne har yanzun muke masu lakabi da cewa su ba sa son kudi sai mulkin. Akwai gidan Sarki Umarun Ndayako, Kakan-kakan Sarki Umaru Sanda da ya rasu, sune mutanan Sakkwato, Gidan Sarki Bello nan ne mutanan Gwandu, don haka yanzun in ka je gidan Sarauta uku za ka taras a Bida. Tun da ake fitintunun nan wannan yana fada da wancan, wancan yana fada da wannan, ka ji ana irin wannan a Bida?
Ni kuwa Kakana Muhammadu Awwalu Bakabe ne, tare suka yi yaki har sai da Turawa suka zo suka ce babu bayi, wanda har yanzun guda daya yana nan a hannun ‘yan baya da mu.

Asalin Garin Kaduna: Nan garin Kaduna garin gwari ne, na san Kaduna a lokacin da babu kowa sai Gwari, Zariya ma garin Gwari ne, ko Amina ba Gwari ce ba. Ni ba abin da ya hada ni fada da Sarakuna, Aminu Kano yana saurayi ya kafa jam’iyyar NEPU, a lokacin muna ‘yan mata a dakin mazajenmu, idan ‘yan NEPU suka shigo gari yakin neman zabe da gudu mazajenmu suke shigowa cikin gida suna cewa ku yi maza ku shige daki ku rufe kofa ga masu zagin Sarakunan nan photo voltaic iso.

Shugabanni irin na yau shawarar ko ka basu ba za su dauka ba, amma ran mutum guda daya in aka kashe, baccin alkawarin Allah ba, da sai Allah ya juye kasar bakidaya, ko ba a taba yi ne ba? don haka ya kamata shugabanni su duba Allah, su kuma duba matsayin da su ma suke a kai kafin Allah ya kai su wannan matsayin da suke a kansa, su duba talakawan da suke a karkashin su. mafiya yawan shugabannin ba su da masu ba su shawara ce tagari, kamar yanda muka ce, ba a mugun Sarki sai mugun bafade. Da yawa in photo voltaic ba su shawarar ba za su je su yi rigingine su yi tunani ba, sai kawai su dauka su kama aiki da ita. Alhalin ba dukkanin mutumin da kake tare da shi ne masoyinka ba, makiyan ma photo voltaic fi yawa a cikinsu.

Addu’ar Musamman Ga Shugaba Buhari: Shugaba Buhari ya nu na zai yi alheri, wallahi an fi karfinsa ne, ya mutum daya zai yi da duk wannan katuwar kasa tamu. Shi kuma Gwamnan garin nan da aka haife shi a kasar Katsinawa, ya tashi da halin Katsinawan, wallahi ka cire wannan halin na Katsinawan daga jikinka ka jefar….(dariya), Allah ya taimake shi, Allah ya dafa masa, Allah ya sa yanda suka hau da bismillahir rahmanir Rahim, su sauka da alhamdu lillahi rabbil alamina. Allah ka nunasshe su hanya madaidaiciya, Allah ba su da karfi, ba su da dubara sai naka, Allah ka yi masu jagora. Don Sayyiduna Muhammdur Rasulullahi (S).

What's On Your Mind?