Bambancin Da Ke Tsakanin Maza Da Mata A Zamantakewa

- Advertisement -

Bambancin Da Ke Tsakanin Maza Da Mata A Zamantakewa

Daga Auwal Muazu

Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta sport da irin wadannan bambance-bambancen.

Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan bambance-bambance kuma su daina tsammanin abokon zaman su su yi aiki yadda suke ji, ma’ana su yi abubuwa kamar yadda suke yi ta fannin tunani da yanayin mu’amala da jinsin da ba nasu ba.

Duk da bambancin ra’ayi da muke da shi, maza da mata na iya taimakon juna ta hanyoyi na ban mamaki matukar dai muna kokari mu fahimci juna kuma mu amince da wadannan kyawawan halaye da kuma rikirkitattun bambance-bambance da muke da su a tsakanin mu.
Na kan ci karo da sakonnin mata akan irin kararrakin da suke kawowa dangane da mazajensu ko samarinsu, wanda rashin fahimtar jinsi ke jawo irin wadannan matsaloli a tsakanin masoya, ga shi suna son juna amma solar kasa fahimtar juna naked har su warware matsalolin da suke fuskanta da juna. Ita mace na son daukar hankali ko kwalliya tayi tana son ta ji an nuna ma ta kulawa tare da yaba kwalliyarta. Ita a tsarin jinsinta a duk inda take tana son a san da zamanta ko zuwanta.

A bangaren mata suna da darajoji daban-daban na halayya. Misali suna daraja soyayya, sadarwa, kyau, da kuma dangantaka. Sannan mata kan dauki tsawon lokaci suna tallafawa, taimakawa, da kula da juna, mafi yawa za ka samu mata solar fi zumunci, tausayi da kuma taimakawa matukar suna da shi.
Ta bangaren maza kuwa suna darajar karfin iko, cancanta, inganci, da nasara. Suna yin abubuwa koyaushe don tabbatar da kansu da habaka karfin su da kwarewar su a kan duk wasu al’amura da suka sa a gaba. Suna bayyana kansu ta hanyar nuna ikonsu don cimma sakamako mai kyau. Suna son duk abinda suka sa a gaba ya zamanto solar cimma nasara da samun daukaka.

Dangantaka ba za ta iya ba kuma ba za ta rayu ba tare da bayyananniyar hanyar sadarwa ba. Idan baku kasance masu gaskiya da aminci tare da abokan zamanku ba to shin dangantakar ku da gaske alaka ce ko kuwa? A duk lokacin da aka samu rashin sadarwa a tsakanin juna sai abubuwa su zama solar koma gefe daya kuma kowane abokin tarayya na iya fara jin kamar dayan baya son ya kasance cikin dangantakar, wadda hakan ka iya kawo rashin jituwa a tsakanin masoya.

Na zanta da mutane biyu dangane da wannan makalar.
Musa: “Ina da budurwar da har yau ina kaunar ta amma ita ta riga tayi assuming cewa ban sonta, ta kasa fahimtar cewa doguwar waya ce da yawan kira ban so. Rashin yi ma ta hakan ya sa mu ka rabu amma ba dan bana sonta ba. Da za ta fahimce mu tsara rayuwar mu ta yanda ni ba ta takura ni haka ita ma ban shiga hakkinta ba. Ta ki fahimtar masu kiranta din ma suna yi ne don ta amince da su da ga an daura aure za su iya komawa ainihin halayyar su”. Saboda haka na ke gani yana da kyau mata su nakalci sanin halin maza wadda hakan zai sa mazajensu su kaunace su matuka ba tare da wani ya takura ba.

Sai wata baiwar Allah da take ban labarin ta “Haka naje gidan kitso da kunshi tun protected sai da yamma na dawo, kuma ya san inda na je amma ko ya ce mu gani, ko ya yi kyau. Har kunshin ya goge kitso ya tsufa bai ce komi ba. Na ji zafin abin sosai haka na share”.
Halayyar maza da mata ta bambanta wajen nuna kulawa da damuwa kowane jinsi da yanda yake nuna na shi.
1. A saukake, maza ba sa jin dadin bayyana abubuwan da suke ji sosai kamar mata, yayin da mata ba sa daukan hakan kamar na maza. Misali, maza suna son a san kwarewar su kuma a yaba musu kuma solar ki jinin a wulakanta su ko kuma a yi watsi da su. A gefe guda kuma, mata suna son a san da yadda suke ji kuma a yarda da su. Maza suna son magance matsaloli da kansu amma mata suna son magance matsaloli a cikin hadin gwiwa a matsayin kungiya. Duk inda mace ke cikin damuwa da zarar ta fadi abinda ke damunta ga makusancinta ta kan ji dadi a ranta ko da bata samu warwarar matsalarta ba. Wasu lokuta maza na iya kallon taimakon da ba a nema ba a matsayin raunin kokarin da suke yi don magance matsaloli su kadai yayin da mata suke daraja taimako, don haka suna kallon hanyoyin da ba a nema ba kamar na neman lalata kokarinsu na ci gaba da hulda. Maza suna son a yaba wa kokarin su na magance matsala, mata suna so a yaba taimakon su koda bai taka kara ya karya ba.
Karanta: Siffofi guda goma da mata ke so a wurin namiji
2. Maza a lokacin da suke fuskantar mawuyacin hali, sukan zama ba sa iya sadar da zance don haka za su iya yin aiki yadda za su taimaki kansu ba tare da solar nemi taimako daga mace ba, yayin da mata su a wannan lokacin suke bukatar a zanta da su a kuma ba su taimako ta hanyar magana ko kuma a aikace.
Lokacin da maza suke magana suna son kaiwa ga kololuwar batun, wato a samu warwarar bakin zaren matsala a take ba tare da bata lokaci ba, amma mata suna jin daɗin magana don kansu.. Solar fi gane warware matsala ta hanyar magana. Misali mace kan shiga matsala idan ta samu yar uwar ta mace da zancen zasu zauna su tattauna kan matsalar na dogon lokaci ba tare da solar warware matsalar ba, kuma ta ji dadi a hakan.
Matukar namiji bai fahimci yadda mace ta bambanta ba, zai iya sa abubuwa su tabarbare lokacin da yake ƙoƙarin taimakawa. Maza ya kamata su tuna cewa mata suna magana sport da matsaloli don kusantowa ba lallai bane su sami mafita.
A mafi yawan lokuta mace kan zauna ta baka labari, ba wai tana neman shawara bane, to da zarar ka katse ta hanyar bata shawara sai a samu sabani.
Maza suna jin daɗi yayin da aka bar su don daidaita lamura da kansu kuma suna jin rauni idan aka nuna ma su tausayi ko taimako yayin da mata ke jin akasin haka. Mata suna jin daɗi ta hanyar ba su tallafi kuma suna jin rauni idan aka bar su su daidaita abubuwa da kansu. Yana da mahimmanci a gane wannan banbancin kuma a tuna shi lokacin da al’amura suka faru a cikin rayuwar zamantakewa.
Kamar yadda mata suke da saurin jin zafin an ki su yayin da basu sami kulawar da suke bukata ba, suma maza suna da saurin jin cewa solar gaza yayin da mace tayi magana sport da matsalolinta, a duk lokacin da mace ke fadin ƙorafin ta sport da wani abu a wannan lokacin sai ta sa namiji ya ji ya muzanta saboda ta nuna gazawar shi ta wannan fannin. Wannan shine dalilin da ya sa tsayawa jin korafi ke ma maza wahalar sauraro a wasu lokuta. A koda yaushe yana son zama gwarzonta a kowane fanni. A duk lokacin da mace ta bata rai ko kuma bata jin dadin komai, sai namiji yaji kamar ya gaza. Mata da yawa a yau ba su fahimci yadda mazan ke da rauni da kuma yadda suke bukatar soyayya ba kamar mata saida su nasu salon daban ne da na mata a mafi yawan lokuta.
Samun kyakkyawan fahimtar juna da sadarwa yana bukatar sa hannun bangarorin biyu. Namiji yana bukatar yin aiki da hankalin shi don tuna cewa yawan korafin mace sport da matsaloli ba ya nufin zargi da kuma dakushe karfin iko na namiji ba. Kamar yadda na fada mace na samun saukin damuwar ta idan ta fada.
three. Maza kamar igiyoyin roba ne. A duk lokacin da suka ja baya, zasu iya mikewa kawai kafin su dawo da baya. Igiyar roba ita ce cikakken kwatancin da za a iya yi da halayya ko dabi’un namiji don fahimtar tsarin jinsin maza. Abin nufi a nan shine wani sa’in maza za su kasance cikin son matsowa kusa wato a irin lokacin ne mace za ta yi wasa da raha da mijinta, akwai kuma lokacin da zai kasance ya ja baya.
Yawancin mata suna yin mamakin sanin cewa ko da namiji yana son mace, lokaci-lokaci yana bukatar ya ja da baya kafin ya matso kusa. A hankalce maza suna jin wannan sha’awar su ja da baya. Ba wai shawara bane ko zabi a’a yana faruwa ne ba tare da masaniya ba. Ba laifinsa bane kuma ba laifinki bane, yanayin su ne ya zo da haka. Wata a duk lokacin da ta fuskanci wannan yanayin tare da mijinta ko saurayinta sai tayi tunanin ko ya daina sonta ne.
Zai iya kaunarta kuma ya amince da ita sannan kuma kwatsam sai ya fara ja da baya. Kamar zaren roba da aka mikar, zai nisanta kansa sannan ya dawo da kansa shi kadai. Namiji ya ja baya don biyan bukatarsa ta ba tare da an takura shi ba.
Yana da kyau kowane bangare kuna dada koyon yanayin bukatocin ku, don sanin su waye ku. Sannan kuma yana da matukar muhimmanci ku karanci su waye dayan jinsin, yanayin dabi’unsu da yanda suke mu’amala da mutane. Ta hakan ne za a samu kyakkyawar fahimtar juna a tsakani ba tare da yawaitar matsaloli ba.

- Advertisement -