A baiwa ‘yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah

0
51

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeder’s Affiliation of Nigeria (MACBAN) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kyale kowane dan Najeriya ya mallaki bindigogi don kare kansa duba da kalubalen tsaro a kasar.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani a kan kalaman da Gwamnan Bauchi, Sen. Bala Mohammed, ya yi cewa makiyaya suna dauke da bindigogi ne kawai don kare kansu.

Gwamna Mohammed ya sha suka sosai bayan goyon bayan makiyaya na yin amfani da AK-47 don kare kansu daga barayin shanu.

Shugaban kungiyar ta MACBAN na jihar Bauchi, Alhaji Sadiq Ibrahim Ahmed, ya fadawa jaridar The Nation a ranar Lahadi cewa babu wani abin damuwa sport da tsayuwar Gwamnan tunda bai ce makiyaya su je su haddasa rikici da shi ba.

A cewarsa, tunda Gwamnatin Tarayya ba za ta iya kare ‘yan kasa ba, yana da kyau kowane dan kasa ya kare kansa daga ‘yan fashi.

Ya ce “Gwamnati ta zama mai rikon sakainar kashi. Hakan yasa Bafulatani ya zama saniyar ware a kasarsa.

A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah

“Dukkanin dukiyarsa ta gurgunta ga satar barayin shanu. Me kuke tsammanin ya yi?

“Kowa ya kare kansa, kowa ya dauki makami. Kada ku bari ‘yan fashi su zo su lalata ku, su kashe ku, su kashe danginku saboda mutane ƙalilan ba za su iya tsoratar da kowa ba.”

Hausawa 3,000 sun fake a gidan Sarki, an birne gawa 11 a kashe-kashen Jihar Oyo

“Ba zan zargi Gwamna Bala Mohammed ba sport da maganarsa, ya yi daidai. Tunda bai ce makiyaya su je su tayar da hargitsi ba.

“Babu wanda ya aibata Gwamnan Benue, Ortom lokacin da ya ce makiyaya su bar jiharsa. Don haka me ya sa suke sukar gwamnan Bauchi?”

A wani labarin, Saleh Alhassan, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure na kasa, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta mayar da martani kan kashe mambobin ta da ake yi a fadin Nigeria.

A tattaunawar sa da jaridar The PUNCH, Alhassan ya yi ikirarin cewa da yawan makiyayan da ake kai masu farmaki da kashe su a fadin kasar, mutane ne da basu ji ba basu gani ba.

What's On Your Mind?