Bai Wa Gwamnati Goyon Baya Ne Zai Bata Kwarin Gwiwar Samun Nasara -Injiniya Amshi

0
142

Shugaban Hukumar Gudanarwar Majalisar Tarayya Nijeriya, Injiniya Ahmad Kadi Amshi, ya ce babu abin da ke tabbatarwa da gwamnati samun nasara kan ayyukan da ta sanya a gaba irin goyon baya dadin kai, Injiniya Amshi ya bayya hakan cikin wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja ranar da aka gudanar da murnar bikin cikar shekara 60 da samun ‘yancin kai wato 1 ga Oktoba 2020 a gidansa dake Abuja. MOBILIZED9JA A Yau Lahadi ta samu damar kawo wannan muku tattaunawa kamar haka;

Ranka ya dade masu karatu za su so su san da wanda muke tare, suna da matsayi.

Suna na injiniya Ahmed Kadi Amshi, Shugaban Hukumar Gudanarwar Majalisar Tarayya Nijeriya.

To Ranka ya dade a yau Nijeriya ta cika shekara 60 cif da samun ‘yancin kai, baya ga mukamin da kake da shi, a matsayinka na dattijo a kasa wane karin haske za ka yi wa ‘yan Nijeriya?

Bai Wa Gwamnati Goyon Baya Ne Zai Bata Kwarin Gwiwar Samun Nasara

Duk abin da za a yi magana a kai babu kamar hadin kai, idan har ba a hada kai ba babu yadda za’ai a ci gaba. Allah ne ya kawo mu tare mu zama ‘yan kasa duka ‘yan Nijeriya. Saboda haka tilas a garemu da ‘yan Kudu da ‘yan Arewa mu hada kai don ciyar da kasarmu gaba. Kamar yadda shi shugaban kasa ya fada, wannan ya zama dole kowa sai ya kawo gudunmawarsa, ba wai a ce wani gefe ne na kasa ne kadai za su gina kasa ba, saboda haka abin da shugaban kasa ya fada ina goyon bayan haka, a bashi goyon baya domin sai an ba wa gwamnati goyon baya za ta samu sukunin aiwatar da abin da ta sa a gaba, saboda mu ciyar da kasa gaba. Wannan kira ne mai muhimmaci ga dukkaninmu, mun sani akwai rigingimu da yawa a kasa amma da yardar Allah duk za mu sha kansu, duk abu ne na fahimta, to mu fahimci juna a shawo kansu mu samu ci gaba a kasa.

Mai Girma Shugaban kasa, ya tabo batun yadda matsalar tattalin arziki ke kara ta’azzara, ya kake kallon abin, kuma wace fuska kake ganin za a shawo kan lamarin?

Tangal-tangal na tattalin arziki ba a Nijeriya ce kadai ba, abu ne wanda duk duniya take fuskanta. Da farko dai sai mu dubi yadda muka tsinci kanmu a cikin wannan lamari na wannan annoba ta cutar Korona, shi ma ya jawo illa sosai sport da tattalin arzikin kasar nan, to kuma ba tattalin arzikin kasar nan ne kadai ba tattalin arzikin duniya ne gaba daya, kuma in Allah ya yarda wannan abu ne mai wucewa.

Ba Mu Da Dan Takarar Kujerar Gwamnan Neja A Zabe Mai Zuwa Sai Injiniya Sani Ndanusa

Amma kafin ta wuce dole ‘yan kasa sai photo voltaic yi hakuri, sai an hada da hakuri za a ga karshensa, sannan sai an ba wa gwamnati goyon baya, akwai hanyoyi da take bi don a ga an kara tattalin arzikin kasa, abin dai da za a ci gaba da gayawa ‘yan kasar shi ne a yi hakuri a ba wa gwamnati goyon baya, domin a yanzu abubuwan da suke na farfado da tattalin arziki ana nan ana ci gaba da su.

Akwai wani kira da za ka yi sport da shawarar da shugaban kasa ya ba wa injiniyoyi da lauyoyi da suke ba da gudunmawa ba a nan kadai ba har a waje, cewa su tsaya ba da gudunmawarsu a na gida?

To wannan shawara da shugaban kasa ya bayar, kira ne mai muhimmanci, saboda kamar yadda ka fada ko ina ka je a duniya za ka samu ‘yan Nijeriya da yawa kwararru a fanni daban-daban suna ba da gudunmawarsu, amma a nan gida muna da matsaloli, matsalolin nan kuwa su ne, na rashin bai wa ainihin kwararrun ma’aikatan ‘yanci da damar yadda za su yi aiki yadda ya kamata.

yawanci muna samun matsaloli daga wurin gwamnati ta yadda ba’a son sa kwararru a inda ya dace, wannan yana daga cikin abin da yake jawo mana matsala a kasar nan. In an san akwai kwarrare yana aiki a waje kaza ya kamata a bashi kulawa a sa shi a inda ya dace, in za mu yi haka, to na waje ma za su yi sha’awar dawowa su kuma na ciki za su zauna a gida.

Kamar yadda muke magana, na san cewa a yanzu haka, tashar jirgin kasa ta Ingila idan injinyoyin tashar jirgin kasa na ingila ‘yan Nijriya suka ce za su dawo Nijeriya, to babu shakka na san tashar sai ta mutu. Saboda gudunmawar da injiniyoyin Nijeriya suke bayarwa, to me ya sa ba za a kawo su su yi a nan ba, wannan gwamnati ya kamata ta tsaya ta yi nazari sosai a kai, ko da yake gwamnati tana nan tana kokari a kan wannan, kwanannan aka ba da ‘yancin kowa ya dawo gida ya ba da tasa gudunmawar, na ciki su ma za su ba da tasu gudunmawar, wannan gwamnatin tana nan tana yi, don haka sai mu ba ta goyon baya domin ganin mun yi nasara a wannan kasa.

Dangane da shirin ba wa matasa dama a wannan gwamnatin, wace irin rawa Gwamnan Jihar ta Yobe ya taka wajen samun nasarar wannan shiri?

To Alhamdulillahi, matasa su ne karfin kasa a ko ina ba a kasar nan kadai ba, duk gwamnatin da ta yi watsi da matasa to ba za ta samu ci gaba ba, domin su ne wadanda kwakwalwarsu take cikin aiki ga su da nagarta, ya kamata a yi amfani da karfin matasan nan kar a barsu su lalace a banza. Alhamdulillahi, Allah ya kawo mu, a Jihar Yobe da kake magana mun samu gwamna da yake kula da matasa. Kuma muna roko a jihar manya da kananan da su bashi goyon baya, idan kuma aka kyale matasa basu da jagora, to fa ba za su yi nasara ba, kasar ma gaba daya ba za ta yi nasara ba. Mun gode Allah mun samu gwamna da yake kula da matasa.

Amma su kuma matasa ya kamata na ja hankalinsu, saboda suna gaggawa kowa yana so ya zama kaza, idan aka kwantar musu da hankali aka nuna musu su ma lokacinsu zai zo, a yanzun ana bukatar su yi amfani da kwakwalwarsu da iliminsu da nagartar da suke da ita su taimakawa kasa, shugabanci Allah zai basu, amma yanzu su daina gaggawa, su bi gwamnati su bata goyon baya.

Amma dai muna godewa Allah da a yanzu haka shi gwamna ya mayar da hankali kan matasa na abubuwa da yake babbasu da ayyuka da yake ta kokarin samar musu, hakan ina mai tabbatar maka zai ga ci gaba a jihar.

A karshe ina kira ga ‘yan kasa gaba daya a kan hadin kai, mu hada kai shi ne babban abin yi, mun san cewa akwai matsaloli a kasar nan, akwai matsalolin tsaro, akwai matsalolin tattalin arziki idan an hada kai duk matsalolin ba za su kara ci gaba ba, amma dai abu muhimmi shi ne a ba wa gwamnati goyon baya, saboda haka ina kira ga jama’a ‘yan Nijeriya da a ba wa gwamnati goyon baya domin ta samu damar cimma nasarar ayyukan da ta sa a gaba.

What's On Your Mind?