Bai Kamata PDP Ta Zargi Gwamnatin Buhari Kan Cin Hanci Da Rashawa —APC

- Advertisement -

Bai Kamata PDP Ta Zargi Gwamnatin Buhari Kan Cin Hanci Da Rashawa —APC

Jam’iyyar APC mai mulkin ta bayyana cewa, bai kamata babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba waje cin hanci da rashawa. Jam’iyyar APC ta mayar da martani ne kan zargin da jam’iyyar adawar take yi na rashin mai da kudaden da tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin ruwan Nijeriya (NPA), Hadiza Bala Usman ba ta dawo da su ba, wanda jam’iyyar ta yi zargin har yanzu gwamnati ba ta yakir cin hanci da rashawa. Jam’iyyar APC ta siffanta kalamun jam’iyyar PDP a matsayin mara tushi ballantana makamai, inda ta ce da gwamnatin ba ta yaki da cin hanci da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai amince wa ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi ya dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, Hadiza Bala Usman ba daga kan mukaminta. Jam’iyyar ta ce, zargin jam’iyyar PDP yunkuri ne na bata gwamnatin da take samun nasarori wajen yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar nan.

A Cikin sanarwar da sakataren ruko na kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar, sanata John James Akpanudoedehe ya shawararci jam’iyyar PDP da ta dunga tatance gaskiyar lamari a kan cin hanci da rashawa kafin ta fito da yi magana a kai.

Ya ce, jam’iyyar PDP ce gidan cin hanci da rashawa wanda ta kwashe tsawan shekara 16 tana gudanarwa a karkashin mulkinta. Har yau jam’iyyar ba ta fahimci yadda wannan gwamna take yakar cin hanci da rashawa ba.

“Gaskiyar magana dai ita ce, gwamnatin jam’iyyar APC wanda shugaban kasa Buhari yake jagoranta ta amince a gudanar da cikakken bincike a hukumar NPA, saboda shi shugaban kasa ya kware wajen gudanar da ayyukan gwamnatin yadda ya kamata. Bugu da kari, shugaban kasa baya lamunta komin karancin cin hanci da rashawa a cikin gwamnatinsa ko kadan.

“Abun kunya ne jam’iyyar PDP ta dunga zargin gwamnatin da cin hanci da rashawa bayan ga ‘ya’yanta can hukumar yaki da cin Hanci da rashawa tana tuhumarsu a kotu na wawushekudade gwamnati a lokacin da suke karagar mulki, shi ne take tunanin ko ‘ya’yan jam’iyyar APC haka suma suke yi. Ba za mu taba iya yin abin da jam’iyyar PDP ta yi ba, muna tabbatar musu da cewa, ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa da miliyoyin nairori da daloli da aka kwato daga mambobin jam’iyyar PDP wanda suka sace lokacin da suke a matsayin jami’an gwamnati, yayin da har yanzu wasu ba a samu nasarar amsowa ba.

“Lallai ‘yan Nijeriya ba za su taba yafe wa wasu jami’an gwamnatin PDP wadanda suka azurta iyalansu da makusantansu lokacin da suke shugabanci. Kamata ya yi jam’iyyar PDP ta mayar da hankali wajen neman gafarar ‘yan Nijeriya bisa irin wandakan da ‘ya’yanta suka yi da arzikin kasar nan wanda shi ne makasudin shigar Nijeriya cikin talauci.”

- Advertisement -