Bagudu Ya Tabbatar Wa Kamfanin Shinkafa Ta WACOT Goyon Baya

- Advertisement -

Bagudu Ya Tabbatar Wa Kamfanin Shinkafa Ta WACOT Goyon Baya

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar wa kamfanin Shinkafa na West African Cotton Firm Restricted (WACOT), goyon baya ga masu zuba jari da ke son saka hannun jari a jihar ta Kebbi a shirye gwamnatin sa ta ke, don bayar da kyakyawar tallafi ga wuraren su a jihar.

“Yana da kyau masu saka jari su sani cewa gwamnatin jihar za ta tallafa musu don samar da aiyuka.

“Mun yi imanin cewa Kebbi wuri ne mai kyau a gare su, saboda ƙarin darajar da kuma goyon bayan da suke ba tattalin arzikin, ” in ji shi.

Sanata Atiku Bagudu ya bayyana hakan ne a farfajiyar masana’antar Kamafanin WACOT da ke garin Argungu, a karamar hukumar Argungu a jiya yayin kaddamar da shirin hadin gwiwar hadin tsakanin USAID da kamfanin Wacot restricted, wanda Ambasadar Amurka a Nijeriya, Madam Mary Beth Leonard ta halarta.

Gwamnan ya ce, ayyukan masana’antar a cikin al’ummar da suke gudanar da ita Shinkafa a Argungu da kuma fadin Jihar ta Kebbi solar gamsu.

Ya nuna farin cikin sa sport da dimbin gudummawar da kamfanin na WACOT ke bayarwa ga bunkasar tattalin arzikin jihar ta Kebbi da kuma Nijeriya baki daya, inda ya bayyana hakan a matsayin daidai da tsammanin masu hannun jari.

Haka kuma Gwamnan, a matsayinsa na Babban Mai masaukin baki, ya yi maraba da Jakadiyar ta Amurka da ayarinta, yana mai bayyana ƙaddamar da haɗin gwiwa tsakanin kungiyar Zuba Jari da USAID da kuma WACOT a matsayin abin da ya dace a kan lokaci, mai matuƙar so da amfanar juna.

“Ban yi mamakin lokacin da USAID ta amince da su a matsayin abokan aiki, muna matukar alfahari da kamfanin WACOT da USAID, saboda suna taka rawar gani a kan nauyinsu, ga masu hannun jari, muhalli da kuma mutunta al’umma,’ ‘in ji shi.

A jawabinta yayin kaddamar da hadin gwiwar zuba jari tsakanin USAID da Kamfanin WACOT, Jakadiyar Amurka, Madam Mary Beth Leonard ta ce, kawancen shi ne na farko daga cikin yarjejeniyoyi bakwai na hadin gwiwar zuba jari da aka fara amfani da karfin kamfanoni masu zaman kansu da zai inganta harkar noma a kasar Nijeriya.
A cewar ta, tallafin Hub din na dala $ 1.5 zai kai tsaye ya tallafawa shirin fadada manoman Shinkafa wato Rice farmers Outgrower, wanda zai baiwa WACOT damar samun karin manoman shinkafa 5,100, wanda rabin su mata ne a cikin shirin.

Ta bayyana cewa, an tsara shirin ne domin inganta rayuwar kananan manoma, fitar da su daga talauci da kuma magance matsalolin rashin abinci da annobar CObID-19 ta haddasa a duniya.

Ambasadar ta ce Kawancen dai, zai samar da sabbin ayyuka dubu eight a cikin ‘yan shekaru masu zuwa kuma tana fatan cewa, yarjejeniyar za ta bude kofofin da za a kara samun hadin kai a nan gaba.

Shugaban kamfanin na Shinkafar WACOT, Alhaji Faruk Gumel, yayin da yake godewa ga Ambasadiyar ta Amurka a kasar Nijeriya, Madam Mary Beth Leonard, da Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu da dukkan baki da suka halarci bikin don kasancewa cikin tarihi don kaddamar da Kawancen Zuba Jari tsakanin USAID da Kamfanin Shinkafar WACOT.

Ya ba da labarin yadda kamfanin shinkafar ya fara tun daga farko a shekarar 2015, zuwa wani yanayi a cikin shekarar 2017, lokacin da kamfanin ya fara aikinsa da kuma kalubalen farko da ya ci karo da su, tare da cin nasara.
A cewarsa, an kafa kamfanin ne a Argungu, Jihar Kebbi saboda dumbin damar wurin.

Ya ce sama da ayyukan yi dubu biyu kamfanin ya samar sakamakon hadin gwiwa da USAID.

Ya jaddada cewa, fadada kamfanin ya ba da dama ga karin samun manoma, wanda noma a kasar musamman noman shinkafa solar yawai ta.

A cewar Gumel, “lokacin da aka kafa kamfanin a shekarar 2017, da wuya muka sayar da kayanmu har tsawon watanni uku, saboda kwastomomin suna neman shinkafar waje.

“Amma a yau, muna sayar da shinkafar Nijeriya ba yadda za a iya hanawa, kuma mutane na ci gaba da neman hakan. Kowa yana son ya zama wakilinmu ga kasuwarmu.”
Tun da farko a nasa bangaren, Mataimakin Shugaban na shirin USAID na Kasuwancin Afirka da Zuba Jari, Mista Karl LittleJohn, ya ce Wacot
za ta samar da ayyuka 60,000 a duk fadin Najeriya da Afirka ta Yamma ta hanyar hadin gwiwar ta da USAID kan aikin fadada wa da inganta noman Shinkafa a jihar kebbi da Nijeriya.

Haka kuma ya ce: “Babban makasudin kafa kamfanin WACOT a Argungu da kuma kaddamar da wannan kawancen a yau shi ne samar da hanyar saka jari da samar da tallafi ga karin manoma.”
LittleJohn ya bayyana cewa, za a samar da ayyukan yi a duk fadin Nijeriya da Afirka ta Yamma.

Ya kara da cewa “Muna so mu nuna cewa za mu iya samar da ayyukan yi. Kuma muna son kara saka jari tare da abokan huldarmu a dukkan kasashen Afirka ta Yamma, inji Shi”.

- Advertisement -