Babu wani fim din da ba za a iya yin sa ba a Kannywood – Darakta Aminu Saira

- Advertisement -

Babu wani fim din da ba za a iya yin sa ba a Kannywood - Darakta Aminu Saira

Fitaccen Darakta Aminu Saira, ya bayyana masana’antar fina-finai ta Kannywood a matsayin masana’antar da har yanzu bai taba ji a ran sa ba cewar masana’antar ta mutu ba. Daraktan ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da fim din sa mai dogon Zango na Labarana da a ke haskawa a yanzu a tashar talbijin ta Arewa 24, in da ya ke cewar ‘abin da na kaddara a raina kuma har yanzu na ke jin sa shi ne, ita masana’antar fim tana nan, sai dai idan wasu solar gajiya, wasu kuma su zo su cike gurbin. Ya ci gaba da cewar “duk da yanzu an samu rauni na kasuwa, wanda hakan ya sa mutane suka daina zuba kudin su saboda asara da su ke yi, to sai kuma Arewa 24 suka shigo suka zo suna yin fina-finan su masu godon Zango, don haka sai mutane suka koma suna kallo, sai dai hakan bai kashe Kannywood ba, sai dai in mutum ne shi a kan sa ya ke ji a ran sa cewar ta mutu.

To kuma ni na sha, fada cewar masu maganar Cewar Kannywood ta mutu ko ba a iya ba duk wani abu ne da masu kallo ne kawai za su ba ka labari, domin wanda ya iya abu ya zo yana kurin ya iya ma wannan ba daidai ba ne, amma dai ni na san babu wani fim na duniya wanda ba za a iya yin sa a Kannywood ba, kawai sai dai idan babu kasafi, duk wani fim na America da ka ke gani wallahi in dai da kasafi kudin sa to za a iya yin sa a Kannywood, saboda Allah ya horewa Kannywood mutane wadanda su ke da kwakwalwa, tun daga matubutan masu bada Umarni, da masu Shiryawar, kawai dai abin da a ke kallo na rauni, to gaskiya rashin kasafi ne. Yanzu ka duba, kamar Mota za ka ga wani ta miliyan daya ya ke hawa, wani ta miliyan biyu da ma sama da haka, iya kudin ka iya shagalin ka, to ita ma harkar fim haka ne, don haka ‘yan Kannywood suna da iyaka na kasafi da kasuwa, babu mamaki da dan fim idan ya yi fim zai iya samun riba ta miliyan biyar, to da zai kasance yanzu ba wannan labarin a ke yi ba, da sai dai ka ga manyan’ yan kasuwa, kamar su Dangote suna zuwa suna zuba kudi a ciki saboda za ka sa miliyan dari biyar ka ci ribar miliyan dari biyar, don haka na ke cewar babu wani fim a duniya da ‘yan Kannywood ba za su iya yin sa ba, sai dai idan babu kasa in kudin da za a yi shi. ”

Dangane da fim din sa kuwa na Labarana, wanda a lokacin da ya yi aikin fim din a ke ganin ya kashe kudin da kamar ya saki maciji a ciyawa kuwa cewa ya yi.”

Innalillahi Wa’inna Illaihirraju’un!! Allah Yasa Mu Cika Da Imani (Tabbas Malam Yayi Gaskiya)

Gaskiya kowa da irin na sa tunanin, domin ni a shekara biyar baya na zauna na yi wannan nazarin shi ya sa a ke so ka rinka tafiya kana kallon yadda rayuwar ka ta ke tafiya domin yau da gobe sai Allah ba mu sani ba za mu kai ko ba za mu kai ba, Amma dai kada mutum ya zauna a waje daya, kullum ka rinka tunanin idan kofa kaza ta Kulle menene mafita? Don haka mun fara shirin Labarana tun kafin a san za a fara duk wani fim mai nisan Zango muka samar da labarin muka fita tsara waje kafin mu fara daukar fim din, to ka ga a lokacin abin da muka dauka duk abin da za ka yi a rayuwa ka bar wa Allah. Don haka ni na yi nazari na ga kasuwar za ta iya Mutuwa, to kuma idan ta mutu menene makoma? Don haka sai na hango kamar gidajen talbijin za su kare ragamar abin, don haka sai na ga cewar bari mu mayar da hankali, wanda daman masu kallon mu suna komawa kallon finafinai masu dogon Zango irin na Indiya da American don haka na ga cewar to me ya sa mu ba za mu zauna mu yi musu irin wannan ba. To da na bincika na ga irin kudi masu yawa da za a iya kashewa, to sai na ga cewar bari mu yi shahada mu yi, dogaro na shi ne na san ko ba dade ko ba jima da yardar Allah za a zo wannan wajen, na gidajen talbijin za su yawaita, yadda za su sayi fim din mu har su mayar mana da kudin mu, kuma a lokacin na yi kasafin fim din har da kasuwar mu, to Amma ka ga wani al’amari na Allah sai ya zama kafin a saki fim din ma kasuwar ta riga ta mutu, kuma da ya ke mun yi abin bisa kyakyawar niyya sai Allah ya kawo mana mafita ya zama an samu in da za a kai shi a nuna shi. ”

Dangane da gidan talbijin din sa kuwa na Saira Film TV, cewa ya yi”ina nan a kan baka na kuma nan gaba kadan daga karshen shekarar nan nortthflixblog ne na wallafa a shafinta.

- Advertisement -