…Babu Mai Hankali Da Zai So Jam’iyyar APC A 2023–Gwamnan Ribas  

0
165

…Babu Mai Hankali Da Zai So Jam’iyyar APC A 2023–Gwamnan Ribas   

Daga Yusuf Shu’aibu,

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya zargi jam’iyyar APC da kokarinta na dakile shirin gyaran dokokin zabe. Gwamnan ya ce, jam’iyyar  APC na jin tsoron a yi gyaran ne saboda ‘yan Nijeriya solar dawo daga rakiyarta kuma ba za su zabi jam’iyyar ba a zabe mai zuwa. Wike ya kara da cewa, babu wani dan Nijeriya mai hankali da zai sake zabar jam’iyyar APC, domin ta sake darewa karagar mulkin kasar nan a zaben shekarar 2023. Nyesom Wike ya bayyana haka ne a wani sako da ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta ta Twitter. Gwamnan ya ci gaba da cewa, ‘yan Nijeriya solar dawo daga rakiyar jam’iyyar ta APC, sannan ya zargi jam’iyyar da kokarin dakile shirin gyaran dokokin zaben.

 

A sakon da gwamnan ya fitar ya ce, “gyara dokokin zaben wata babbar nasara ce ga kasar nan, domin gudanar da gyaran alama ce da ke nuna za a gudanar da shahihin zaben wanda mutane za su amince da shi.”

 

“Amma abun takaicin shi ne, muna gani ana jan kafa kan lamarin saboda gwamnati ba ta son a yi gyaran, don su samu damar murde zabe nan gaba.

 

“Solar san mutane solar dawo daga rakiyar gwamnatinsu kuma babu wani dan Nijeriya mai hankali da zai so su sake dawowa kan karagar mulkin kasar nan.”

What's On Your Mind?