Babbar Magana:- Wata Mata Ta Zubawa Yarinyar Da Aka Bata Riko Ruwan Zafi Da Barkono A Gabanta

0
125


Babbar Magana Wani Rahoto Da Jaridar Tribune On-line Ta Ruwaito, Ya Nuna Yadda Wata Mata Dake Zaune A Yankin Iyara Cikin Garin Warri Dake Jihar Delta Ta Batawa Wata ‘yar Uwarta Gaba.

Matar Wacce Ta Aikata Laifin A Ranar Alhamis Ta Zubawa ‘yar Uwartan Wacce Take Zaune Da Ita Ruwan Zafi Da Barkono A Gaba Akan Zargin Da Take Na Cewa Yarinyar Tayi Lalata Da Wani.

Dalilin Haka Ya Sanya Mutanen Yankin Suka Kama Matar Wacce Aka Boye Sunanta Zuwa Sakatariyar Matasa, Inda Aka Umarceta Akan Ta Kai Yarinyar Asibiti Wacce Take Ta Ihun Kuka Sakamakon Zafi Da Radadi Dake Damunta A Gabanta.

Daga Baya Kuma An Ruwaito Cewa Ba A Kai Wannan Lamari Hannun ‘yan Sanda Ba, Saboda A Yanayin Dokar Wannan Yanki Lamari Irin Wannan Ana Shawo Kanshi A Tsakanin Al’ummar Yankin Ne.

What's On Your Mind?