Babbar Cibiyar Shuka ’Ya’yan Itatuwa Dake Kusa Da Kogin Rawaye

- Advertisement -

Ma Wenming, shi ne mai kula da manyan rumfunan shuka ‘ya’yan itatuwa dake kauyen A’yihai a yankin Hainan dake lardin Qinghai. Ya ce, cikin wadannan manyan rumfuna, ana shuka pitaya a galibin gonakin, domin pitaye shi ne ‘ya ‘yan itatuwa na farko da aka shigo da su cikin kauyen, shi ya sa, suna da kwarewa wajen shuka pitaya sosai.

Babbar Cibiyar Shuka ’Ya’yan Itatuwa Dake Kusa Da Kogin Rawaye

A shekarar 2016, Ma Wenming ya halarci wani kwas na horaswa kan ayyukan gona a birnin Zhangye na lardin Gansu, cikin wannan kwas, ya yi mamaki kwarai da gaske ganin yadda ake noman pitaya sosai a birnin. Sa’an nan, ya yi nazari kan yanayin kasa dake tsakanin kauyensa da birnin Zhangye, yana ganin cewa, yanayin wuraren biyu suna kama da juna, shi ya sa, ya fidda wannan ra’ayi na shuka pitaya a kauyensa.

Lekki Shooting: CSOs knock Presidency for rejecting Amnesty International’s report

A shekarar 2017 kuma, ya fara shuka pitaya a babbar rumfa ta gidansa, sa’an nan, ya fara girbi pitaya a shekarar 2018. Wannan nasarar da ya cimma, ya sa ya zuba jari Yuan dubu 400 wajen gina manyan rumfuna guda 7 domin shuka pitaya.

Bisa kokarin da shi da uwargidansa suka yi, pitayar da suka shuka photo voltaic fara yin suna a sassa daban daban, hakan ya sa, photo voltaic sayar da dukkanin pitaya da suka fitar. Ma Wenming ya ce, a bana, ya sami kudin shiga har Yuan dubu 400 ta hanyar sayar da pitaya.

Yanzu, ya fara samar da guraben ayyukan yi ga masu fama da talauci a wurin, kowane mutum zai iya samun kudin shiga Yuan 3600 a kowane wata, lamarin da ya samar da wadata ga karin mutane masu shuka pitaya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

- Advertisement -