Babban Albishir Ga Wadanda Suke Cikin Tsarin N-power

0
193

Babban Albishir Ga Wadanda Suke Cikin Tsarin N-power

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kammala shirin sake daukan matasan da suka yi aiki a shirin N-POWER shiga wani sabon tsarin shirye-shirye (Empowerment Program), ta hannun babban bankin Nigeria (CBN)

Matasan dake N-POWER rukunin batch “A” da “B” sune kawai za’a dauka a shirin domin basu dama a wurare daban-daban da CBN ya tsara, an kammala gwajin web site din, anyi masa suna da “Nexit Portal”

Za’a fitar da Web site din nan ba da jimawa ba dan matasan da sukai N-POWER su shigar da bayanan da gwamnatin take bukata daga gare su, kamar yadda ma’aikatar bayar da tallafi karkashin jagorancin Minista Hajiya Sadiya ta fitar da bayanin.

Nuhu Abdullahi Zaiyi Aure Mecece Makomar Fati washa?

Wadanda suka yi N-POWER kadai ne, kamar yadda sunan web site din ya tabbatar da haka wato “NEXIT PORTAL”, kamar ana nufin “N-POWER EXISTED PORTAL”, sai aka takaice shi da “NEXIT” ko “N – EXIT”.
Wannnan yana zuwa ne kwanaki kadan masu zuwa da za’a sake sunayen wadanda suka cika N-POWER batch “C” wadanda suka yi nasara watan December nan Insha Allah.

Bayan kammala aikin N-POWER a rukunin batch A da B, shugaba Buhari yaga dacewar gwamnatin sa ta cigaba da rike matasan, domin samar musu da hanyoyin samun kudi a cikin shirin da ya tsara na fitar da mutane miliyan dari daga talauci nan da shekara goma masu zuwa Insha Allah

Maigirma Shugaba Buhari yana fatan cigaba da samar wa matasa hanyoyin samun kudi, duk da adawar da ake yiwa gwamnatin sa mai zafi ta ko’ina. -Barr. Abdulhadi Isah

Yaa Allah Ka kara taimako da yin agaji ga shugaba Buhari, Ka raba tsakaninsa da azzalumai maciya amana Amin mun dauko daga shafin datti assalafy.

What's On Your Mind?