DHQ: Ba’a samu galaba akan sojoji ba, abinda ya faru a Marte dabara ce da salon yaki

0
24

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta musanta rahotannin kafafen yada labaran da suka bayyana cewa an samu galaba akan rundunar sojin Najeriya yayi harin garin Marte.

A ranar 15 da 16 ga watan Janairu ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Janar John Enenche, shugaban sashen yada labari na rundunar tsaro ta kasa, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP solar kai farmaki sansanin soji da ke wajen garin Marte, amma an dakile harin.

Ba'a samu galaba akan sojoji ba, abinda ya faru a Marte dabara ce da salon yaki

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito Enenche na cewa dakarun soji solar kashe dumbin mayakan tare motocinsu na yaki guda 13.

“Wasu labarai na nuna Kamar an murkushe dakarun soji yayin harin, wanda hakan ba gaskiya bane.

ABIN AL’AJIBI!| An Yanke Wutar Gidan Tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari Saboda Bashi

“Solar fara kaddamar da harin ne ta wani shingen binciken ababen hawa da ke kusa da wani gidan mai.

“Dakarun soji da ke wurin dole su janye jikinsu kamar yadda aka koya musu a dabarun yaki.

“Ba guduwa suka yi ba, solar yi hakan ne da gan-gan domin zuko ‘yan ta’addar zuwa wurin da za’a yi musu rubdugu.

“Kuma hakan ce ta faru a lokacin, solar fada tarko, don kafin su ankara tuni sojoji solar sanar da sojojin sama domin kawo musu agaji.

“An kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addar tare da lalata motocinsu na yaki guda 13 a karshen harin da suka kai ranar,” a cewarsa.

Enenche ya bayyana cewa rundunar soji ta matukar kassara ‘yan ta’adda a jihar Borno domin yanzu basu da katabus kamar yadda suke da shi a baya.

Legit.ng ta rawaito cewa a ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa rundunar jami’an tsaro ta ‘Thunder Srike’ ta kaddamar da harin kwanton bauna akan wasu ‘yan bindiga a yankin karamar hukumar Kagarko.

Mista Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, ya sanar da cewa jami’an tsaro solar kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar a cikin jawabin da ya fitar.

A cewar Aruwan, rundunar jami’an tsaro ta samu nasarar kaddamar da harin ne a daren ranar Litinin a kan hanyar Sabon Iche zuwa Kagarko.

What's On Your Mind?