Ba Za Mu Yarda CBN Ya Ci Gaba Da Hana Shigo Da Masara Ba – Masu Kiwon Kaji

- Advertisement -

Ba Za Mu Yarda CBN Ya Ci Gaba Da Hana Shigo Da Masara Ba – Masu Kiwon Kaji

Daga Abubakar Abba,

Wasu masu kiwon Kajin gidan gona a kasar solar nuna  ja da matakin Babban Bankin Nijeriya CBN na ci gaba da wanzar da haramta shigo da Masara  cikin kasar.

Solar  yi nuni da cewa,  ci gaba da harmtawar, zai shafi kokarin da ake yi na watada kasar da abinci mai yawa da kuma  shafar masana’antun kasar da ke yin sana’ar.

A  hirarsu da jaridar  Nigerian Tribune,  masu kiwon wadanda suka  bukaci a sakaya suna yinsu, solar bayyana cewa,  makin na bankin, wata makarkashiya ce ta daga wa  manyan dillalan  da ke shigo da ita,  musamman manyan da suka fito daga daya daga cikin yankin kasar.

Ya ce, hakan  zamo babban nakasu ga  dimbin masana’antun kiwon,  musamman kanana da suka dogara kan Masara wajen   tafiyar da masana’antun  su .

A cewarsu, “Babu wani dalilin da zai sa a haramta shigo da Masara cikin kasar,  inda kuma suka kara da cewa,  dakatar da ahigo da ita cikin Nijeriya, zai dakushe kokarin da ake yi na wadata kasar da abinci mai yawa,  musamman da kuma ci gaba da zama nakasu ga fannin na kiwon Kajin”.

 

Solar bayyana cewa,  daukacin fadin duniya da kuma ita kanta Gwamnatin Tarayyar,  suna sane da cewa  sama da kashi  80  na manoman da ke a Nijeriya,  solar kauracewa  gonakansu  saboda ayyukan mahara,  rikicin Fulani Makiyaya da Manoma wanda hakan ya janyo kashe- kashe, fyade da sauransu.

A cewarsu, “In ba dan ba a barnata wa Fulani Makiyaya Rugagen su ba,  da  Nijeriya  ta kasance a matsayin kasar da za ta kasance mai wadataccen abinci”.

Solar yi nuni da cewa,  sai hakan sabanin yadda lamarin yake me a yanzu a kasar,  musaman ganin manoman da suka ci bashin aikin noma a kasar,  solar gaza biyan bashin da suka karba .

A cewarsu,  “ Manoman da dama,  bankuna na binsu bashi,  inda kuma da damansu,  barayin Shanu da kuma masu garkuwar da mutane suka  hallaka  wasun su da kuma mayar da wasun su nakasassu”.

Solar danganta tsarin na bankin  CBN na haramta shigo da Masara cikin  a  matsayin tsari mayar kayu,  inda suka jaddada cewa,  wata shiryayyar harkala ce kawai,  ta bai wa wasu shafaffu masu kudi da ke a wani yanki  kasar  damar shigo da ita domin samun kazar riba.

Solar yi nuni da cewa,  ko Masarar da CBN ya fitar a kwanan baya, domin samar da dauki ga masana’antun kiwon Kajin a kasar,  da tada aka wayarwa da masana’antun.

“Tun da ba za mu iya noma ta da yawa ba a kasar  ba,  kamata ya babban bankin na CBN ya dage haramcin shigo da ita cikin Nijeriya domin  ci gaba da karancinta a kasar,  na matukar shafar  masana’antun kiwon Kajin,  nusamman ganin yadda karancin ke ci gaba da zama barazana  ga kasuwancin”.

- Advertisement -