Ba Za Mu Taba Siyasantar Da Rayukan ‘Yan Nijeriya Ba– APC

0
114

Ba Za Mu Taba Siyasantar Da Rayukan ‘Yan Nijeriya Ba– APC

A ranar Litinin ce a garin Abuja, jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa ba za ta taba siyasantar da rayukan mutane ba, sai dai ta inganta jindadin da walwalar ‘yan Nijeriya. Sakataren roko na jam’iyyar APC, Sanata John Akpanudoedehe shi ya bayyana wannan tabbaci a cikin bayaninsa na rashin tsaro a wasu bangarorin kasar nan. Ya bayyana cewa, rashin tsaro yana kara ta’azzara wanda ya hada da ayyukan ‘yan kungiyar Boko Haram da na ‘yan bindiga da na masu garkuwa da mutane domin amsar kudin Fansa da na ‘yan fashi da makamai wanda yake ci gaba da faruwa a wasu jihohin kasar nan.
Ya kara da cewa a ‘yan kwanakin nan, jam’iyyar APC ta mayar da hankali ya gaba daya wajen bankado wadanda suke haddasa rashin tsaro da masu daukan nauyinsu, domin gurfanar da su gaban kuliya tare da yanke musu hukuncin kamar yadda doka ta tanada. Haka kuma, Akpanudoedehe ya bayyana cewa, jam’iyyarsu tana ci gaba da mayar da hankali da ci gaba dukkan yankunan kasar nan.
“Jam’iyyar tana iya bakin kokarinta duk da irin rashin tsaron da ake fama da shi a kasar nan, muna kira da a hada kai wajen dakile rashin tsaro a Nijeriya.
“Kasantuwar tsaro ne kadai zai iya sa a samu nasarar shirin noma wanda zai sa Nijeriya ta sami shinkafa kanta da sauran kayayyakin abinci.
“Samun tsaro ne kadai zai sa mu ji dadin ababan extra rayuwa da aka samar na gyaran hanyoyi da hanyar tarayya da aka gina wacce takai kilomita 13,000 da daukacin gidace da aka gina,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, ‘yan Nijeriya ba za su fada tarkon masu son zuciya ba wadanda suka dai-daita harkokin tsaron kasar nan. Akpanudoedehe ya ce, lamura irin wadannan baban hatsarin ne da tsaron kasa. Ya ce, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta goyan ta’addanci kuma ba ta nuna bambanci. Sakataren jam’iyyar ya ce, shugaban kasa ya samar da sababbin shugabannin tsaro ne domin ceto kasae nan da kuma tsaftace rashin tsaro da ake samu. Ya ce, akwai bukatar ci gaba da samar da tsaro a kasar nan da samun hadin ka, domin samun damar aiwatar da aikin da tsarin mulki ya tanada na tsare rayukan da dukiyoyo da kuma kare martabar kasarmu.
“Ya kamata mutane su dunga taimaka wa gwamnatin wajen sauke dauyin da ya rataya a wuyata na kare kasar nan tare da bayar da bayanan mutane da bamu yarda da su ba ga jami’an tsaro.
“Gwamnatin shugaba Buhari za ta ci gaba da karfafa samar da kayayyakin tsaro a dukkan daukacin jihohin kasar nan domin samar da tsaro,” in ji shi.
Sakataren riko na jam’iyyar APC ya ce, ya kama ‘yan kasa su hada kai wajen yaki da rashin tsaro a cikin kasar nan.

What's On Your Mind?