Ba Za Mu Janye Yajin Aiki Ba Sai An Biya Mana Bukatunmu -Shugaban PTD  

0
91

Ba Za Mu Janye Yajin Aiki Ba Sai An Biya Mana Bukatunmu -Shugaban PTD  

Ba za mu janye yajin aikin gama gari da muka tusnduma ba Har, sai iyayen gidanmu na Kungiyar NATO photo voltaic biya mana bukatunmu. Shugaban Kungiyar  Direbobin Tanka PTD, reshen Jihar Kaduna Kwamarede Abdulrahim Haruna ne ya yi wannan kalaman cikin hirarsa da manema labarai a ofishinsa da ke jihar Kaduna, kan yajin aikin da ‘ya’yan kungiyar suka tsunduma na kasa baki daya.

Kwamarade Abdulrahim wanda aka fi sani da Abudullahi 63 ya ce,  “Tun makonni uku da suka gabata, mun bayar da sanarwa ta gargadi kan shiga yajin aikin, inda muka umarci direbobinmu su sanya ganye a jikin motocin da suke tukawa har zuwa sati biyu tun daga ranar farko har zuwa makonni biyu, kuma har kwanukan suka cika babu daya daga cikin shugabannin iyayen gidanmu da suka zo suka similar mu don fara tattaunawa dangane da wannan yajin aiki da nufin sulhu.”

ASUU ta janye yajin aikinta na tsawon wata tara a Najeriya

Abudullahi 63 ya ci gaba da cewa, “Mun yi iya bakin kokarinmu domin a yi sulhu,  amma abin ya ci tura, muka kara basu mako guda ko Allah zai sa photo voltaic zo a sulhunta ba.

A cewar Abudullahi 63 ya ce,  “Bamu da wata hanya da za mu iya kwatar wa kanmu ‘yanci illa mu ajiye masu motocinsu, muna aiki da yunwa ba ma iya cin abinci, mutanenmu ana korarsu daga gidajen da suke haya, ‘ya’yansu ba sa iya zuwa makaranta, sannan kuma direbobinmu in photo voltaic yi tafiya photo voltaic bar matansu a gida ba sa iya cin abinci, kuma hatta gwamnatin ta ja hankalinsu kan su biya mana bukatunmu domin su ma direbobinmu su ci gaba da walwalar, amma photo voltaic ki”.

Daga cikin bukatun da ya ambata, “Muna bukatar karin albashi da alawus-alawus, domin abin da a ke biyan mu daga nan Kaduna zuwa Legas,  bai wuce naira 10,000 ba wasu masu a cikinsu, su kan biya Naira 15,000, alhali direba na da mata daya da ‘ya’ya, sannan kuma in direba ya yi tafiya zai je ya yi kwana bakwai ko 10, kuma ko da ya bar wa matarsa 15,000 ba za su iya riketa har da ‘ya’yansu har zuwa tsawon kwana 10 kafin ya je ya dawo ba. Kuma shi ma direban, dole sai ya rike wanda zai ci abinci a hanya a cikin kudinsa da yaron motar”.

“In wata ya kare, albashin direban bai wuce Naira 30,000 ba wanda ya dade,  ya na aikin shi ne ake bai wa Naira 40,000, a saboda da haka,  ba za mu janye yajin aikin ba har an biya mana bukatunmu tukunna”.

What's On Your Mind?