Ba-ta-kashin Binuwe: Gwamna Ortom Na Farfaganda Don Bai Son Biyan Albashi – Fulani

- Advertisement -

Ba-ta-kashin Binuwe: Gwamna Ortom Na Farfaganda Don Bai Son Biyan Albashi – Fulani

Yadda Gwamnan Ya Yi Gudun Fanfalaki Na Fiye Da Kilomita daya A kafa

Ortom Ya Nemi A Cafke Shugabannin Fulani
Gwamna Kuma Wike Ya Yi Zargin Da Ya Saba

Al’ummar Fulani a Jihar Binuwe sun yi zargin cewa, Gwamnan jihar Mista Samuel Ortom yana yada farfaganda a kansu ne kawai, don ya batar da hankalin al’umma da ma’aikatan jihar ta yadda zai ji dadin kin biyan albashin ma’aikata a watan nan.
Idan dai za a iya tunawa, a yammacin ranar Asabar ne Gwamnan Jihar Binuwe, Samuel Ortom, ya tsallake rijiya da baya tare da jami’an tsaronsa, lamarin da ya kai shi ga ya arta cikin na kare, domin tsira da ransa sakamakon farmakin da wasu ’yan bidigan da ba tantance ko su waye ba suka kai masa.
Gwamnan, wanda aka yi zargin ’yan bindiga sama da 15 ne suka farmake shi a gonarsa dake Tyo-mu akan hanyar Makurdi zuwa Gboko, ya nemi a cafke tare da gurfanar da shugabanin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, wadanda ya yi zargin suke neman rayuwarsa ruwa a jallo biyo bayan wata ganawar baya-bayan nan da aka yi a garin Yola ta Jihar Adamawa.
Sai dai kuma fa, tsohon Shugaban na Miyetti Allah a jihar ta Binuwe, Garus Gololo, ya sanya kafa ya shure zargin Gwamna Ortom din da cewa, kawai ya shirya farfagardarsa ne, domin neman damar da zai kauce wa biyan ma’aikatan jihar albashinsu a karshen watan nan na Maris.
Ita kuwa jam’iyyar da Ortom ya ke, wato PDP, ta yi tir da Allah wadai da yunkurin hallaka mamban nata, sannan ta bukaci hukumomin tsaro da su bankado tare da kamo dukkanin wadanda suke da hannu a wannan yunkurin.
Da yake yi wa ’yan jarida bayanin yadda ta kaya da shi daki-daki a garin Makurdi, Gwamna Ortom, ya bayyana cewar, ya yi gudun fanfalaki ne da kafarsa, domin ceto rayuwarsa daga maharan, domin gudun da ya yi na tsawon kilomita guda a kasa ya yi shi.
“Na gode wa Allah da ya sanya akwai kuzari a jikina, wanda har ya ba ni damar yin gudun tsira da rai na tsawon kilomita daya da rabi ba tare da na tsaya ba. Abun nufi a nan, Allah ne kawai ya ba ni ikon da dama kuma cike nake da godiya a gare shi.”
Gwamnan ya kuma bayyana dogaransa a matsayin wasu jaruman da suka bada kokari wajen dakile shirin ’yan bindiga sama da 15 da suka bude wa tawagar tasa wuta da suka nema daukar rayuwarsa.
A daidai lokacin da jami’an tsaronsa suka tunkari maharan tare da maida musu da martani, Ortom sai ya ce, a wannan gabar ne ya hango fili fetal, inda kawai sai ya tsinke a guje a sukwane, domin neman dai tsirahar tsawon kilomita daya da rabi.
Kalmominsa na cewa, “cike nake da godiya da jinjina wa zaratan jami’an tsaron da suke aiki a karkashina. Sun samu damar maida martani sosai wanda hakan ne ma ya sanya masu harin ba su samu damar isowa gareni ba.
“Cike nake da godiya wa Allah bisa ba ni karsashi da kuzarin gudu har na tsawon kilomita daya da rabi ba tare da na tsaya ba. Abun nufi a nan, Allah ne kawai ya bani ikon da dama kuma cike nake da godiya a gare shi.
“Ni a zahirance ban da matsala da kowane Bafulatani ko kabilar Fulani a jumlarsu. Sai dai gaskiya Ina da matsala da Fulani masu dauke da bindiga wadanda suka sha alwashin sai sun mamaye Nijeriya domin ta zama musu gida. Na kuma ce. A matsayina wanda nake jagorantar jihata.
“Idan har ni gwamna ba zan iya zuwa gonata dauke da jami’an tsaron da ke kare rayuwata ba, waye kuma zai iya zuwa gona? Ku yi tunanin irin radadin da muke ji a nan jihar Binuwe.
“Godiya ga Allah da ya sanya shugaban kasa da ya amsa wasikata duk wanda aka gani da bindiga AK-47 kawai a harbeshi. Har zuwa yanzu dai ban ga wanda aka harba bisa wannan umarnin ba. Ina fatan zan ga hakan ya faru a jihar Binuwe.
“Na kai rahoton wannan lamarin ga hukumomin tsaro ina kuma fatan hakan zai faru domin tsarkake muhallanmu da jama’anmu domin ba su damar komawa gonakai da zuwa wuraren aiki ba tare da fargabar rasa rayuka a kowani lokaci ba.
“Ina kira ga shugaban kasa, hukumomin tsaro da su fiddo da wadanda suka yi wannan aika-aikar. Suna nan yanzu haka a cikin daji tsakanin Makurdi da Abinse.
“Su na rayuwarsu sannan suna fitowa su zo su aikata ta’addancinsu da yin fyade wa mata, su kashe mana mutane, tare da jikkata jama’anmu, su tarwatsa da lalata mana gonakai, suna yawonsu a kogi daga baya su koma cikin daji.”

*Sanin Lungunan Gonar Ne Suka Taimaka Wa Ortom Ya Tsira Da Rayuwarsa, Cewar Ganau:
Wani ganau ya lura kan cewa arcen na kare da kuma sanin lunguna da sakona gonaar da gwamna Ortom ya yi ne suka taimaka masa wajen tsira da rayuwarsa.
Ganau din, ya kuma ce, gwamnan da hadimansa na tsaro sun shiga babban gonar ne da kafarsu bayan sun ajiye motocinsu a wuri mai nisa da gonar.
Ba a shiga gonar da motocin ba ne sakamakon yanayin rashin kyan hanya da kuma ganin motocin ba za su ji dadin shiga gonar ba.
Cikin rashin sani a garesu, maharan sun buya cikin daji ba tare da sanin gwamna ko jami’an tsaronsa ba.
An iya gano cewa a wannan yanayin na zagayen cikin gonawa ne maharan suka samu damar farmakar gwamnan da ruwan harsasai.
Bayan samun nasarar maida martani da jami’an tsaron da tsirar da shi, sojoji sun mamayi gonar inda suka tabbatar da sun fatattalin ‘yan bindigan daga yankin.
Wani babban jami’i na cewa: “A ranar Asabar gwamna ya samu lokaci ya je gonarsa da ke kan hanyar Makurdi-Gboko. Sakamakon gargadar hanyar gonar motocin gwamnan da na jami’an tsaronsa sun faka a kan hanya tare da yin tattaki zuwa cikin gona.
“A lokacin da suke tattalin zagayen gona ne masu harmakin wadanda tunin sun buya cikin gona, suka bude ruwan alburusai wa gwamnan da ‘yan tawagarsa.
“Ortom ya arci na kare na tsawon kilomita daya, domin lamarin ya faru a daidai lokacin da duk motocin su na fake a waje.
“A tunani sanin da gwamnan ya yi wa gonar ne ya taimakesa tsira daga wannan mutuwar da ta dumfaroshi.
“Da yiyuwar masu harin sun yi ta bibiyar tsare-tsare da shirye-shiryen yau da kullum na gwamnan wanda hakan ne ma ya ba su damar farmakarsa,” inji ganau.
Ganau din ya bayyana cewar gonar gwamnan dai babba ce wacce yake shuka ababen amfanin gona daban-daban a ciki.

PDP Ta Yi Tir Da Neman Halaka Ortom:
Jam’iyyar da gwamna Ortom ke ciki, PDP, ta yi tir da Allah wadai da harin da ta kira na ganganci da yunkurin kasheshi wanda ake zargin ‘yan bindiga dadi ne suka aikata.
PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi duk mai yiyuwa domin tabbatar da ganowa da cafko wadanda suka kitsa wannan danyen aikin.
A sanarwar da jam’iyyar ta fitar, ta kuma nuna kaduwarta da damuwarta kan wannan dayen aikin.
Sanarwar na PDP na cewa: “@OfficalPDPNig ta nuna damuwarta bisa kokarin dauke rayuwar gwamna Ortom don haka muke neman ‘yan Nijeriya da su daura alhakin duk abun da ya faru da matsalolin tsaro kan @OfficalAPCNg da ke mulkin kasar a halin yanzu domin alhakin tabbatar da tsaro na kan gwamnati mai ci.”
Daga nan jam’iyyar ta nemi Ortom da cewa kada wannan lamarin ya sanyaya masa guiwa ta nemi ya dage kana ya kara kaimi domin cimma nasarar da ya sanya a gaba wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar.

Gwamnatin Tarayya Ke Da Alhaki Muddin Ran Ortom Ya Salwanta – Gwamna Wike:
Gwamna Nyesom Wike ya shaida cewar gwamnatin tarayya ce za ta dauki alhaki muddin aka kashe Ortom.
Ya ce, kashe gwamnan Binuwe zai kara jefa Nijeriya cikin wani yakin basasa.
Wike a sanarwar manema labarai da babban mai taimaka masa kan hulda da ‘yan jarida, Kelbin Ebiri ya fitar na cewa, “Dukkanin wani abun da ya samu gwamnan Binuwe za mu dauka alhakin ne ga gwamnatin Nijeriya.”

Surutan Ortom Cike Suke Da Farfaganda – Tsohon Shugaban Miyyeti Allah:
Tsohon shugaban kungiyar Miyyeti Allah a jihar ta Binuwe, Garus Golo, ya zargi gwamnan da kokarin wawantar da hankalin jama’a don guje wa biyan albashin ma’aikata a karshen wata.
Yana mai cewa ikirarin da gwamnan ya yi na cewa an farmakesa shadi-fadi ne kawai don samun guri.
Garus wanda ke bayani wa majiyarmu, ya shaida cewar a kowace watan da gwamnan ke neman kin biyan albashi sai ya bijiro da wani batun da zai dauke hankalin jama’a daga batun albashi.
Ya ce, “Babu wasu makiyaya a wannan yankin da yake magana a kai.
“A garin Makurdi na taso. Kawai abun da na fahimta shine, gwamnan a duk karshen wata san ya bijiro da batun Fulani makiyaya domin ya karkatar da hankalin ma’aikata.
“Kusan shekaru biyu kenan ana fama da matsalar albashi, shekaru kusan uku bai biya fansho ba.
“Kawai matsalarsa shi makiyaya. Ina tunanin yau 20 ga wata ko, to yana neman uzurin da zai hanasa biyan albashin ma’aikata a karshen wata ne.
“Fulani makiyaya ba su da wata kullalliya da Ortom.”
Ya zargi gwamnan Ortom da rashin gudanar da ayyukan raya jiharsa illa fakewa da batun Fulani kawai ya sanya a gaba.

- Advertisement -