Ba Ni Da Alaka Da Jirgin Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga – Janar Abdulsalam

- Advertisement -

Ba Ni Da Alaka Da Jirgin Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga – Janar Abdulsalam

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Tsohon shugaban kasa a karkashin mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa ba shi da alaka ko miskala zarratin da wani jirgi da aka ce an kama yana kai wa ‘yan bindiga abinci da makamai a cikin dazuzzuka.

Abdulsalami ya musanta hakan ne ta bakin mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Dakta Yakubu Sulaiman, a wata takardar manema labarai da ya raba. A takardar an bayyana cewa labarin na kanzon kurege ne da ba shi da tushe balle makama.

A cikin rahoto da ke yawo a kafofin sadarwa na zargin an kama wani karamin jirgin sama da ke kai wa ‘yan bindiga abinci da tallafin makamai wanda a ciki kafofin sadarwar suka danganta jirgin da tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar.

Mai magana da yawun nasa ya ce tsohon shugaban kasar ya yi watsi da ire-iren rahotannin, kuma yana so ya tabbatar da gaskiyar lamarin bisa sakamako na gaskiya.

Ya ce Janar Abdussalam ya nesanta kan shi da irin wannan laifin da ake danganta ‘yan kasa na gari da shi.

“Irin wannan labarin na kanzon kuregen da ake yadawa da bai inganta ba, jami’an tsaro suna sanya ido a kan duk abin da ke faruwa a kasa kuma ba za su sanya ido ya cigaba da kasancewa ba. Yana mamakin yadda mutum zai zauna ya kirkiri irin wannan labarin da zai bata kimar mutum.” A sanarwar.

Tsohon shugaban kasar, ya jawo hankalin al’umma da su yi watsi da wannan labarin kuma ya nemi masu yi su guji kirkirar labaran da ba su inganta ba suna watsawa a shafukan intanet.

Ya janyo hankalin ‘Yan Nijeriya da su cigaba yin aiki tare wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a kasa.

- Advertisement -