Ba Mu San An Kori Kowa Aiki Ba – Ishaku Yakubu

- Advertisement -

Ba Mu San An Kori Kowa Aiki Ba – Ishaku Yakubu

Daga Mustapha Abdullahi, Kaduna

Duk da labaran da ke yawo na cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta sallami wasu ma’aikata, Shugaban kungiyar ma’aikatan Jinya da unguwar Zoma ta kasa reshen Jihar Kaduna, Ishaku Yakubu, ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa su a matsayinsu na masu aikin Jinya da unguwar Zoma a Jihar da suka kai akalla mutum 2500, ba su ma san wai an Sallami wadansu daga cikin ‘ya’yansu aiki ba.

Ishaku Yakubu ya shaida wa manema labarai hakan ne a Kaduna, inda ya ce su a matsayinsu ba su na rokon wani ya dauke su aiki ba ne, “neman m ake yi a wadansu jihohi a duk fadin Nijeriya, amma wadanda suke wannan aikin su a matsayinsu na shugabanni kullum su na kokarin ba abokan aikinsu ne hakuri su zauna a Kaduna domin Jiharsu ce za su yi wa aiki su taimakawa yan jiharsu, domin ana nemansu a ko’ina ciki har da wajen Nijeriya”, inji Ishaku.

Ishaku Yakubu ya ci gaba da cewa ba a cikin gidan rediyo ko Talbijin aka dauke su aiki ba, akwai hanyoyin da aka bi aka dauke su aikin, don haka sai an bi tsarin yadda ya dace idan ana son sallamar ma’aikaci irinsu da ke da matukar muhimmanci a wajen kula da lafiyar al’ummar kasa baki daya”.

Ya ce “abubuwa uku na shaida wa shugabannin asibitin Barau Dikko da suka kira ni taro a ranar Litinin da ta gabata. Na gaya masu cewa ba aikin ‘ya’yan kungiyar da nake yi wa shugabanci ba ne su kulle kofar shiga asibiti, wannan sai wadanda aka dauka aikin gadi.

Na biyu na gaya masu cewa ba aikin ‘ya’yan kungiya ta ba ne su Sallami duk wani majinyaci da ya je asibiti neman a lafiyarsa. Sai kuma na uku cewa ba gaskiya ba ne wata ma’aikaciyar jinya ta cire wa wani yaro na’urar taimaka masa ya yin numfashi wannan ba gaskiya ba ne ko kadan”.

“A lokacin da muka samu wannan labarin cewa an cire wa yaro na’urar da ke taimaka masa yin numfashi mun kafa bincike domin tabbatar da gaskiya, inda muka bi iyayen yaron har asibitin da suka kai shi sakamakon yajin aikin da aka fara, mun kuma je asibitin har wasu ‘yan jarida solar tattauna da uwar yaron ya na nan da ransa kuma ta fadi gaskiyar lamari, wanda ya zuwa yanzu haka yaron nan na nan da ransa kuma har iyayensa solar dawo da shi asibitin Barau Dikko domin ci gaba da nema masa lafiya,” In ji shugaban.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “masu yin aiki irin na mu ana neman mu ne a ko’ina cikin duniya, kowace rana masu aikin jinya da unguwar Zoma na ficewa daga Nijeriya zuwa wadansu kasashe ana kuma daukarsu aiki da makudan kudi masu tsoka, haka abin yake a wasu jihohi”, inji Ishaku.

Ya kara da jaddada cewa solar shirya neman Hakkinsu na kokarin bata masu suna a matsayinsu na ‘ya’yan kungiyar masu aikin jinya da unguwar Zoma a duk fadin Jihar Kaduna da ya hada da dukkan kananan Hukumomi 23, da muke da mambobi dubu 2500 da suke kula wa da lafiyar jama’a.

- Advertisement -